Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Manhajar TikTok ta koma aiki a ƙasar Amurka bayan wani ɗan lokaci da aka sanar da dakatawa.
Kafar ta sada zumunta, wadda ta Chana ce, ta gode wa Donald Trump, wanda ya ce zai yi ƙoƙari ya warware batun da ya jawo matsalar tun a farko. Sama da Amurkawa miliyan ɗari da saba’in ne ke amfani da TikTok.
Kamfanin ya ce zai yi aiki tare da Trump don samar da mafita ta dogon lokaci don ci gaba da kasancewa a Amurka.
A kwanakin baya ne dai Kotun ƙoli ta Amurka ta tabbatar da dokar haramta amfani da manhajar TikTok a ƙasar, sai dai idan kamfanin da ya mallaki manhajar, wato ByteDance, ya amince ya sayar da manhajar kafin 19 ga watan Janairu.
Kamfanin ByteDance, na China, ya ƙalubalanci dokar kuma ya musanta cewa yana saɓa dokar kare ’yancin tofa albarkacin baki kan masu amfani da manhajar su fiye da miliyan 170 a Amurka.
Sai dai Kotun ƙolin ya yi watsi da ƙalubalantar hukuncin da kamfanin ya yi, wanda hakan ke nufin wajibi ne manhajar TikTok ɗin ta samu mai sayenta da aka amince da shi domin samar da manhajar samfurin Amurka ko kuma ta fuskanci dakatarwa.
Hukumomi a Amurka da ’yan majalisu sun zargi kamfanin ByteDance da alaƙa da gwamnatin China kuma sun bayyana manhajar a matsayin barazana ga tsaron ƙasar.
Hanyar da ake ganin Amurka za ta haramta TikTok ita ce ta hanyar umurtar rumbun manhajoji, kamar ‘Google play store’ da ‘Apple store’ su cire manhajar a Amurka, ta yadda babu wanda zai iya sauke ta a wayarsa.
Hakan na nufin mutane ba za su iya bin hanyoyin da aka amince da su wajen shiga manhajar ba – duk da dai hakan kuma na nufin mutanen da suka riga suka sauke manhajar, za ta ci gaba da kasancewa a kan wayoyinsu.
Sai dai kuma waɗanda ke da manhajar a wayoyinsu kafin haramta ta ba za su iya sabunta ta ba, wanda hakan za zai sa manhajar ta lalace ta yadda ba za a iya amfani da ita ba.
Hakazalika, sabunta manhaja na taimakawa wajen toshe matsalar masu yin kutse a manhaja, a dalilin haka idan mutane ba za su iya sabunta ta ba, zai bai wa masu kutse damar kutsawa cikin wayoyin miliyoyin mutanen da ke amfani da manhajar.
Tabbas akwai hanyoyi da dama da masu amfani da manhajar za su bi domin tsallake shingen haramcin.
Tuni aka fara wallafa hoton bidiyo, wanda ya karaɗe shafin na TikTok da ke ilmantar da masu amfani da shi yadda za su yi amfani da VPN( Virtual private network) – wata hanya da za ta bai wa mutum damar nuna kamar yana wani yankin ne na daban.
