Dalilin da ya sa muka ƙara farashin man fetur – Matatar Ɗangote

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

A ƙarshe dai matatar man Dangote ta bayyana dalilin da ya sa ta ƙara farashin man fetur.

A cewar kamfanin man, matatar ba ita ce ke ɗaukar nauyin ƙarin da aka yi a baya-bayan nan kai tsaye ba.

Hukumar kula da matatar mai mai ƙarfin tace gangan 650,000 a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa ci gaban yana da nasaba kai tsaye da gagarumin ƙarin farashin ɗanyen mai a duniya, tare da bayyana cewa duk wani sauyin da aka samu a farashi na ƙasa da ƙasa babu makawa zai yi tasiri ga farashin mai a ko ina.

Sanarwar ta ƙara da cewa, matatar ta fahimci muhimmancin arahan man fetur ga ’yan Nijeriya, tana mai bayyana ƙudurin ci gaba da bayar man fetur mai inganci.

 “Yayin da muka yi gyare-gyaren kashi 5 cikin 100 a kan tsohon farashimmu daga N899.50 zuwa N950 kan kowace lita, yana da kyau mu lura cewa wannan ƙarin ya yi ƙasa sosai fiye da hauhawar farashin ɗanyen mai da kashi 15 a duniya, wanda hakan ya sa fetur mai inganci ya samu. ɗanyen man fetur ya tashi daga dala 70 zuwa dala 82 a cikin kwanaki kaɗan, baya ga kuɗin da ake samu a kasuwannin duniya.

By ukarofi