Ɓatanci: Osimhen ya maka ɗan jaridar Turkiyya a kotu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ɗan wasan gaba na Super Eagles, Victor Osimhen ya shigar da ƙara akan ɗan jaridar Turkiyya da ya zarge shi da yi masa duka a wani wajen cin abinci mako biyu da suka gabata.

Abokin Osimhen na ƙud-da-ƙud kuma ma’aikacin gidan rediyo, Onokala Onyebuchi da ake kira da Buchi Laba ya bayyana hakan a shafin X, ranar Lahadi.

Ya ce Osimhen ya maka ɗan jaridar ne a kotu bisa zargin sa da yi masa duka.

Haka kuma ya ce za a fara shari’ar ne a ranar Talata.

Hakan na zuwa ne a lokacin da Bozduman ya zargi ɗan Nijeriyar da casa shi bayan kammala wasan da ƙungiyar Galatasaray ta yi 3-3 tsakaninta da Dynamo Kyiv a farkon watan nan.

Ɗan jarida Bozduman ya yi ikirarin cewa Osimhen cikin fushi ya kai masa naushi a lokacin da ya yi yunƙurin ɗaukar hoto tare da ɗan wasan a bayan filin da aka yi wasan.

Rahotonni sun yi zargin cewa Osimhen ya biya kuɗi don a ba shi ɗaukar inda lamarin ya faru saboda a goge ta a matsayin hujja.

Ɗan wasan mai shekaru 26 ya musanta zarge-zargen da ake masa inda ya bayyana su a matsayin ƙarairayi.

By Babaji