UNICEF ta haɗa hannu da ƙungiyar likitocin ƙananan yara don bunƙasa kiwon lafiya A Gombe

Spread the love

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe

Shugabar Ofishin UNICEF na Bauchi, Dakta Nuzhat Rafique, ta jaddada ƙudirin hukumar na cigaba da yin haɗin-gwiwa da Kungiyar Likitocin Kananan Yara ta Najeriya (PAN) don bunƙasa harkokin kiwon lafiya da cigaban yara a ƙasar.

Dakta Nuzhat ta bayyana hakan ne yayin da ta shiga cikin wajen jerin gwanon tattaki da likitocin suka gudanar, tafiyar da ta fara daga ƙofar Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III zuwa filin wasa na unguwar Pantami inda aka mayar da hankali kan manufofin UNICEF da PAN na tallafa wa lafiyar yara.

Da ta ke magana da manema labarai, Dakta Nuzhat ta bayyana cikakken goyon bayan UNICEF ga taron, inda ta ce “Ƙungiyar Likitocin Yara na daga cikin manyan abokan UNICEF. Mu na da manufa ɗaya kan yara, waɗanda su ne abinda aka mayar da hankali a wannan taron”, inji ta.

Ta bayyana ce taron ya kuma ƙunshi ayyuka da bitoci da aka shirya don bunƙasa lafiyar yara, musamman na haihuwa da shayar da yara nono zalla.

“An gudanar da bitoci kan yadda za a farfaɗo da jarirai da suka fuskanci matsalar numfashi, da tallafin numfashi ga yara. Wadannan ayyuka suna da matukar muhimmanci wajen inganta rayukan yara da kuma gina wata sabuwar al’umma mai lafiya a Najeriya.”

Kazalika ya ta yaba da ƙoƙarin likitocin wajen bunƙasa kiwon lafiyar yara da tsira ga jarirai, tana mai cewa wannan yana da muhimmanci ga ci-gaban ƙasa.

By Babaji