Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara, tayi barazanar ɗaukar matakin shari’a bisa dakatar da shugaban marasa rinjaye kuma ɗan majalisar jihar mai wakiltar mazaɓar Talatan Mafara ta Kudu, Hon Aliyu Ango Kagara da majalisar ta yi ƙarƙashin jagorancin kakakin ta Hon. Bilyaminu Ismail Moriki tayi.
A wata sanarwa ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na jihar Yusuf Idris a ranar Laraba a Gusau, ta bayyana matakin da ‘yan majalisar dokokin jihar suka ɗauka a matsayin abin kunya, cin zarafi da kuma yunƙurin kawar da jam’iyyar APC daga majalisar dokokin jihar.
Majalisar a zamanta na ranar Talata, 28 ga watan Janairu, ta bayyana kujerar ɗan jam’iyyar mu a matsayin korarre saboda abin da suka kira rashin zuwa zaman majalisar amma ba komai bane illa dalilai na siyasa don rufe bakin ‘yan adawa a majalisar, wannan muna Allah wadai da shi gaba ɗaya ”.
Muna ƙalubalantar shugaban majalisar bisa yadda ya dakatar da wasu mambobi tara daga majalisar a ranar 8 ga watan Janairun shekarar 2024, ba tare da bin ka’idar kundin tsarin mulki ko ƙa’idojin majalisar ba, sannan an hana dukkan albashi da alawus-alawus na ’yan majalisar da abin ya shafa don bayyana ra’ayinsu kan ƙalubalen tsaro a gaban majalisar wanda ya zama laifi ga shugabancin majalisar”.
Saboda son zuciya da gangan suka manta cewa a shekara biyu majalisar ta zauna wata 2 kacal domin a cikin watanni huɗun farko suna hutu, yayin da sauran watanni shida ke nan kuma ba su zo ba, amma idanuwan sun rufe suka ayyana korar ɗan majalisa Aliyu Ango Kagara wanda aka zaɓe shi a majalisar a karo na huɗu, bayan haka, kafin a ayyana ko cire kowane mamba, akwai buƙatar bin kundin tsarin mulki da wasu matakai waɗanda dole ne a bi su ba sanarwa ta gungun mutane ba.
“Jam’iyyar APC tana buƙatar majalisar dokokin ta bayyana wa al’umma sau nawa suka zauna domin zartar da hukunci mai inganci a zauren majalisar a shekaru biyu da sukayi ba kawai su taru cikin ɗan ƙanƙanin lokaci domin ganawa cikin sirri sannan kuma a ɗauki wannan matakin ba”.
Yusuf ya bayyana cewar duk wani ɗan majalisa da aka samu ya saɓawa ka’idar majalisar, dole ne a yi masa shari’a ta adalci kafin kowane mataki, ba wai matakin rufe ido da ‘yan majalisar sukayi ba na ɗaukar matakin rashin adalci”.
Hakazalika, jam’iyyar APC ta yi kira ga majalisar dokokin jihar da ta bada umarni a kan lamarin don dawo da zaɓaɓɓun ‘yan majalisar da suka dakatar ko Kuma su ɗauki matakin zuwa kotu don neman haƙƙin su.
