Daga MUHAMMADU MIJITTABA a Kano
Shugaban Kamfanin Sadarwa na KABS kuma shugaban riƙon ƙungiyar kasuwar waya ta Beirut Road da ke Kano, Ambasada Kabiru Musa ya bayyana cewa kafin wannan lokaci da kyar ake biyan ma’aikatan wannan kasuwa albashi a kowane wata, wanda hakan ce ta sa duk ƙarshen wata, sai an bi rumfa-rumfa, gida-gida, ana harhaɗa kuɗi a kasuwar don biyan ma’aikatan tsaron kasuwa da tsaftace ta kamar dai yadda Ambasada Kabir Musa ya bayyana a ganawarsa da manema labarai a ƙarshan makon nan.
Haka kuma ya ce “amma cikin ikon Allah da aka bashi wannan riƙo a kwana biyar ya samu kuɗin da zai biya ma’aikata albashi, haka kuma ya faru ne sakamakon toshe hanyoyin zirarewa kuɗin ƙungiyar da ta ke faruwa a baya musamman idan aka yi la’akari da cewa wannan kasuwar, kasuwa ce ta matasa kashi 95 na 100 matasa ne a kasuwar domin dattawan da su ka kafa wannan kasuwar ko sun koma ga Allah ko kuma sun barwa yara, wannan kuma shi ne dalilin da ya sa babu wuru-wuru, babu cuwa-cuwa, a wajen cin kasuwar Beirut da ke Kano, ga kuma albarka da Allah ya yi wa kasuwar.”
Kuma ya ƙara da cewa ba da daɗewa ba ƙungiyar za ta gabatar da zaɓan shugabanni cikin kwanciyar hankali da ikon Allah.
A ƙarshe ya ce kaɗan daga cikin nasarorin da mu ka samu, ni da masu taimakamun shi ne, Sanya ma’aikatan wannan kasuwa a ƙalla 50 cikin shirin inshora na kula da lafiya na taimake ke niyar lafiya na gwamnatin kano da ake kira KSCHMA Kuma an ƙara musu albashi wanda a baya dubu 18 ake biyan su, amma bisa la’akari da tsadar rayuwa ta ke aka ƙara musu wani kaso mai tsoka a albashin su kasancewar su masu kula da dukiyar al’umma wanda sakamakon ziyara ta bazata da na ke kawowa a wasu lokuta ne, na gano ma’aikatan wannan kasuwa ba na ganin wasu, idan na tambaya sai a ce wannan rashin lafiya ne, shi ne ya sa na saka su a wannan tsari na kula da lafiya ta hanyar taimakekeniya tsakanin gwamnati da al’umma baki ɗaya, inda kuma ya yabawa Alhaji Abba Kabir Yusuf kan kulawarsa da harkokin kasuwanci da sauran fannoni na rayuwar al’umma da cigaban Kano a dukkan manufofin gwamnatin Kano.
