Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Yusuf, ya bayyana damuwarsa kan cewa kashi 30 ne kacal na mata a Jihar Kano ne ke haihuwa a asibiti, wani al’amari da ke bada gudunmawa wajen yawaitar mace-macen mata masu juna biyu a jihar.
Ya jaddada cewa yawan mace-macen mata masu juna biyu a Nijeriya ba abin abinda za a amince da shi ba ne.
Dakta Yusuf ya yi wannan bayani ne a ranar Litinin yayin wani taron bita da aka gudanar a Bristol Palace a Kano mai taken “Matakin Rage Mace-Macen Mata Masu Juna Biyu da Jarirai.”
Jaridar Tribune ta rawaito Kwamishinan na bayyana cewa, “Dole ne mu haɗa kai domin tabbatar da cikar burin gwamnatin tarayya na rage mace-macen mata masu juna biyu a ƙasar nan.
“Jihar Kano tana da muhimmanci sosai idan aka yi la’akari da alamu na ɓangaren kiwon lafiya da kuma matsalolin da ke addabar wannan ɓangare.
“Domin Kano, wacce ita ce jiha mafi yawan jama’a a ƙasar, ana samun yawan mace-macen mata masu juna biyu da jarirai, wanda ya hana ni da gwamna samun barci tun lokacin da muka hau kan mulki,” inji Yusuf.
A cewar Kwamishinan Lafiya, gwamnatin Jihar Kano a ƙoƙarinta ta ƙirƙiro da tsarin bayar da kulawar haihuwa kyauta ga mata masu juna biyu tare da samar da kayan aiki ga sama da cibiyoyin kiwon lafiya 60 da kuma cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko guda 63.
