Ƙungiyar ɗalibai ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin mako biyu ta gyara titin Numan zuwa Jalingo

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ƙungiyar ɗalibai ta Nijeriya (NANS) ta bayyana hanyar Numan zuwa Jalingo dake Jihar Taraba a matsayin tarkon mutuwa tare da bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 da ta gyara hanyar.

Lucky Emonefe, Shugaban NANS na ƙasa, ya bayar da wa’adin ne a ranar Asabar da ta gabata a Jalingo, Babban Birnin Jihar Taraba, yayin bikin ƙaddamar da majalisar zartarwa ta shiyyar Arewa maso Gabas na ƙungiyar, ya kuma yi gargaɗin idan gwamnati ta kasa fara aikin titin, za su gudanar da zanga-zangar gama gari.

Shugaban ya ce, ƙungiyar za ta mayar da sakatariyarta ta ƙasa daga Abuja zuwa Arewa maso Gabas matuƙar gwamnatin tarayya ta kasa fara aikin titin bayan ƙarewar wa’adin.

Ya bayyana hanyar a matsayin ɗaya daga cikin mafi munin titunan ƙasar nan, inda ya bayyana cewa halin da hanyar ke ciki na barazana ga rayuwar ‘yan Nijeriya ciki har da ɗalibai.

“ƙungiyar ɗaliban Nijeriya ta ƙasa ta kafa dokar ta-ɓaci a hanyar Jalingo Numan. Hanyar na ɗaya daga cikin mafi muni a Nijeriya kuma tarkon mutuwa ce ga ’yan Nijeriya, musamman ɗalibai, musamman a shiyyar Arewa maso Gabas.

Emonefe, ya yi kira ga ma’aikatar ayyuka ta tarayya da ta umurci ɗan kwangilar da ke kula da aikin gyaran hanyar da ya gaggauta komawa wurin ya fara aiki domin ceto rayukan ‘yan Nijeriya da ke bin hanyar.

Shugaban ya yaba wa gwamna Agbu Kefas na Taraba bisa manufofinsa na kyautatawa ɗalibai a jihar tare da bayyana gwamnan a matsayin gwamna mafi son ilimi a Nijeriya.

“Muna farin ciki kan manufofin ɗaukaka darajar ilimi da gwamnan jihar Taraba ya ɓullo da shi da kuma aiwatar da tsarin ilimi kyauta da kuma rage kashi 50 na kuɗaɗen karatu na manyan makarantu a jihar.

“Mun shawarci sauran gwamnonin da su yi koyi da kyawawan ayyukan da Gwamna Agbu Kefas yake yi, musamman a fannin ilimi, wanda shine jigon ci gaban kowace al’umma,” inji Shugaban NANS.

Tun da farko a nasa jawabin sabon kodinetan NANS na shiyyar Arewa maso Gabas, Mista Umar Afkawa, ya ce burinsa shi ne inganta jin daɗin ɗalibai a shiyyar.

By ukarofi