Mu daina raina mata ko yara akan hikima

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ

Daya daga cikin manyan malamai a tarihin Musulunci, wato Hassanul Basri, ya bada labarai guda biyu cewa:

1. Wata rana sai ya hango wani yaro ya doso shi ya na riƙe da wuta wadda ya cunno ta na ci, sai ya ce da yaron, “kai ina ka samo wannan wuta haka?” Ai kuwa sai yaron nan ya yi wuf ya hure wutar ya ce min, “ya kai Hassan, gaya min inda wutar ta tafi, ni kuma sai na gaya maka inda na samo ta.”

2. Wata rana ina zaune sai ga wata kyakkyawar mace ta zo wajena fuskarta ba hijabi, don kawo ƙarar mijinta. Ta na fara magana sai na katse ta, “Malama, fara rufe fuskarki tukuna kafin ki ci gaba da bayani.” Sai ta kada baki ta ce, “yi haƙuri Malam Hassan, cikin ɗimauta na rasa inda hankalina ya shiga, ban ma san cewa fuskata a buɗe ta ke ba. Ba don ka ankarar da ni ba, sai ma na shiga kasuwa a haka. Amma kuma kai da ke da matuƙar kusanci da Ubangiji Allah bai kamata a ce ka kawar da idanuwanka yadda ba za ka san cewa ko fuskata a rufe take ko a buɗe ba?”

Wannan magana ta shige can cikin ƙahon zuciyata. Wannan abu da wannan mata ta yi shine ya yi cikakkiyar fassarar ayoyin Suratul Nur, domin Allah sai da ya umarci maza da kautar da idanuwansu a aya ta 30 kafin ya umarci mata a aya ta 31 da su rufe jikinsu, wanda ma babu fuska a ciki.

Don haka jama’a kafin ka yanke wa wani hukunci fara yankewa kanka, kuma mu guji raina mutane, saboda wani dalili na jinsi, launi, asali, rashin wadata ko ƙarancin shekaru wajen yanke wa mutane hukunci kafin mu fahimci manufarsu.

ɗaya daga cikin aikin da falsafa ke koya mana shine tarbiyantar da tunaninmu. Allah ya ƙara mana hikima.

Malam Ali Abubakar Sadiƙ manazrci mazaunin Kano

By ukarofi