Gwamnatin Katsina ta raba kayan noma na Naira biliyan takwas

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

A ƙoƙarin ta na inganta noman rani a jihar, gwamnatin Katsina ta rabawa ƙananan hukumomi 34 kayan noma da kuɗin su yakai Naira biliyan takwas.

Shugaban ƙaramar hukumar Mani Dr Yunusa Mohammad Sani ya faɗa wa manema labarai haka a ofishin sa.

Ya bayyana cewa kayan sun haɗa da garman shanu na zamani da injiunan ban ruwa masu amfani da hasken rana da buhu 13,000 na takin zamani da maganin feshi da sauran su.

Ya ce gwamnatin jihar ta rabawa kowace ƙaramar hukuma garmunan shanu guda ɗari da injunan ban ruwa masu amfani da hasken rana.

Dr Yunus ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta sayi kowane garmna ɗaya akan Naira miliyan ɗaya amma ta saida akan Naira 150,000 domin sauƙaƙa wa manoma a jihar.

“Haka kuma gwamnatin jihar Katsina ta sayi tare da raba wa mata tunkiya guda ɗari a kowace ƙaramar hukumar”.inji Dr Yunus

“A tsarin rabon tunkiyar kowa ce mace aka bata tunkiya guda huɗu a matsayin rancen wanda tsarin biyan shine da zaran tunkiya ta haihu ya’yan zasu zama na gwamnati”ya bayyana haka.

Shugaban ƙaramar hukumar ya kuma yi bayani akan wasu aikace-aikace da ƙaramar hukumar ta aiwatar a tsawon mulkin su .

Ya ce sun gyara makarantu da azuzzuwa na firamare a garuruwan Dubi ta kusheyi, Bagiwa,Tsagen,Maku,Magani.

Dr Yunus ya ce hukumar ta tallafawa ilimi mata na majalisar dinkin duniya AGILE ta kashe Naira biliyan ɗaya wajan makarantu guda shida tare da samar da kayan karatu a makarantun.

By ukarofi