Majalisar Dokokin Kano ta amince da ƙirƙirar rundunar tsaro mai ɗauke da makamai

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Majalisar dokokin Jihar Kano ta amince da wata doka da zata kafa rundunar tsaro ta jiha domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Bayan muhawara mai zafi kan wasu sassa na dokar, majalisar ta amince da tanadin da ke hana duk wani wanda ke cikin jam’iyyar siyasa jagorantar rundunar.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Hon. Lawan Husaini Dala, ya bayyana cewa an yi nazari sosai kan dokar don tabbatar da cewa tana amfani ga kowane ɓangare na jihar.

Sabuwar dokar ta ba wa jami’an rundunar ikon ɗaukar makamai, cafke masu laifi da kuma hana aikata miyagun ayyuka a faɗin Kano.

Dala ya tabbatar da cewa wanda zai jagoranci rundunar dole ne ya kasance ba ɗan wata jam’iyyar siyasa ba, kuma ya zama ɗan asalin jihar Kano.

By ukarofi