Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Ga wanda bai san AES ba, sabuwar ƙungiyar ƙasashe uku ne da ke ƙarƙashin mulkin soja a yankin Afurka ta yamma. Wannan ya biyo bayan juyin mulkin soja da sojoji su ka yi a ƙasashen da su ka haɗa da Jamhuriyar Nijar, Mali da Burkina Faso. ƙasashen 3 ba su ƙara ƙarfi ba sai lokacin da sojoji su ka kifar da gwamnatin farar hula ta Muhammad Bazoum a Nijar. Matakin da ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Afurka ta yamma ECOWAS ta ɗauka a lokacin na buƙatar sojojin ƙarƙashin Janar Abdulrahman Thiani su maida mulki hannun farar hula ko in sun ki za a duba yiwuwar amfani da ƙarfin soja wajen dawo da Bazoum kan karaga. Bayan kin maida mulkin, Nijar ta sha takunkumi daga ECOWAS ciki da katsewa ƙasar lantarki. Daga bisani an janye takunkumin kuma tawagar malamai da ta shiga Nijar ta samu nasarar dakatar da yaƙi ko amfani da ƙarfin soja kan sojojin da ke ikirarin sun zo aikin ceton Nijar ne daga ‘yan ta’adda. Da alamun gudun haɗa kai da ECOWAS don za ta iya shata lokacin da za a maida mulki hannun farar hula ya sa sojojin da a zahiri ba su da lokacin sauka daga mulki, ƙasashen uku sun kafa wata ƙungiya da su ka laƙabawa suna AES don aiki tare da kuma ɗangarewa daga ECOWAS. Musamman sauran shugabanni biyu na sojan daga Mali da Burkina Faso sun shigo Nijar don mara baya ga Janar Thiani. Al’ummar Nijar mafi rinjaye na matuƙar kaunar kifar da gwamnatin Bazoum da maida martani mai zafi ga duk wanda ke kiran a dawo da mulkin hannun farar hula ko aƙalla a saki Bazoum ya ma fice daga ƙasar. In mun tuna Bazoum wanda tsohon shugaban Nijar Muhammadu Issoufou ya tsayar takara ya lashe zaɗe ko an aiyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɗe bayan zagaye na biyu na zaɗe tsakanin sa da tsohon shugaban ƙasar Muhammad Ousmane. Haƙiƙa akasarin ‘yan Nijar musamman ‘yan uwa baƙar fata ba sa mara baya ga Bazoum ya zama shugaba don kasancewar sa mai asali daga Larabawa. An ma yaɗa kamfen cewa Bazoum ba ma asalin dan Nijar ba ne. Wato gaskiyar magana duk yanda mutum zai kalli abun ba zai kore shigowar hamaiyar jinsin bakake da farare ba. Ai mun tuna yadda turawa su ka bautar dabakar fata a Afurka ta kudu kafin ‘yan gwagwarmaya ƙarƙashin marigayi Nelson Mandela su karɗi ragama da samun haɗin kan tsohon shugaban ƙasar de Klerk wanda zuwa yanzu shi ne jar fata na ƙarshe da ya mulki ƙasar. Ba lallai irin hakan ya faru a Nijar ba amma siyasa ta kawo ƙin jinin dangin su Bazoum da a ka ba da alƙaluman ba su fi kashi 5% na al’ummar kasar ba. Ba za a yi mamaki ba inda Muhammad Ousmane ya lashe zaɗen sojojin nan ba za su samu goyon bayan da su ke samu yanzu ba ta yadda komai su ka fada sai ka ji goyon baya ko ta ina. Idan mutum bai yi dogon tunani ba zai fahimci ya auka son zuciyar sa ba kuma ya kamata a san cewa soyayya hana ganin laifi. Idan ka na matukar son abu ko mutum in ba adalci ka daure ka yi ba to duk laifin da ya yi ba z aka gani ba. A kan samu soyaiya ko kiyaiya mai zafi a dalilai fitattu uku da su ka hada da ƙabilanci, bambancin addini da kuma ɗangaranci. Haƙiƙa-haƙiƙa sai fa mutum ya zauna shiru shi kaɗai ya yi dogon tunani kafin ya gano shin bai dimauce da son zuciya bisa abubuwan nan uku ba? In kuma ka ga mutum ya samu irin wannan dogon nazari amma bai samu sauyin tunani ba to soyaiya ko kiyaiya ta hanyar son zuciya ta yi kanta a zuciyarsa. Wanda irin wannan kanta ta cinye zuciyar say a rube lugub cikin mayen yaudarar kai sai dai a yi ma sa addu’a ko kawai a fita harkar sa don kuwa ba ma wani abu da zai dauwama sai sarautar Allah mahaliccin sammai da ƙassai.
Jamhuriyar Nijar ba bakuwa ba ce ga akasin juyin mulki amma kowanne na da na sa tsarin. Ai ma mun tuna yadda a ka sojojin su ka kifar da ɗan uwan su Janar Baare Mainasara su ka kuma bindige shi har lahira. Mun tuna yadda sojoji su ka kawar da marigayi shugaba Tandja Mammadou. Ba ɗaya daga juyin mulkin da a ka a baya a Nijar da ya samu irin goyon bayan da na wannan karo da Thiani ya haye madafun iko. Shin ko za mu yi nazari mu gano dalilai? Shin sojojin za su iya kawar da ‘yan ta’addan da su ka ce barin su, su ka yi ƙarfi ya kawo su? ko ma dai yaya tsinke alaƙar ƙud da ƙud da Faransa ba shi kaɗai ne zai ceci al’ummar Nijar daga matsalar tsaro ko mulkin mallaka ba. Wato ko yanzu ‘yan Nijar su ka daina kowace alaƙa da Faransa ƙasar ta turawan yamma ta riga ta yi wa ‘yan Nijar illar sauya mu su ɗabi’u zuwa irin na turawa. Hatta yadda wasu ‘yan boƙon Nijar ke tafiyar takama ko sanya kaya irin na Turawan Faransa ne. Yo in har Faransanci ne harshen gwamnatin Nijar ai an ki cin biri ne an sha romon sa. Shin akwai burin wasu ‘yan Nijar da ya wuce tafiya birnin Faris?. Kai Faransa ta yi raga-raga da al’adun gargajiya na al’ummar Nijar. Wannan yanayi ya sa wasu ba sa dogon tunani wajen kushe duk wanda ya ci karo da ra’ayinsu ko da kuwa a tarihi dan uwan su daga yankin arewacin Nijeriya. Ai ni in na gamu da dan Nijar wallahi gani na ke yi ɗan uwa na ne kuma raba iyaka da turawa su ka yi bai raba wannan zumuncin ba. Amma cusa ɗabi’ar turawa ta wariya tsakanin ƙasashen Afurka mulkin Faranshi da na Ingilishi ya kawo illa ainun da ko an farga ba za a iya kawar da kantar illar ba sai dai a rage kaifin ta bayan kowa ya ga uwar bari.
Gwamnatin Nijeriya ta ce ta yi duk abun da ya dace don dakatar da Jamhuriyar Nijar, Mali da Burkina Faso daga ficewa daga ƙungiyar ECOWAS amma yunƙurin ya ci tura.
Wannan na zuwa ne bayan ƙarewar wa’adin ficewar ƙasashen a watan nan na Janairu duk da ECOWAS ta kara sabon wa’adi na tsawon wata 6.
Kazalika ƙasashen sun ƙaddamar da matakin buga sabon fasfo don jingine amfani da na ECOWAS da kan ba wa ‘yan ƙasashen ƙungiyar damar zagawa ba shamaki.
Ministan harkokin wajen Nijeriya Yusuf Tuggar ya ce sun dau duk matakan ‘yan uwantaka da diflomasiyya don jan hankalin ƙasashen su zauna da dangi amma ba sakamako mai ƙarfafa guiwa “ba irin ƙoƙarin da ba a yi. Ni din nan na yi yunƙuri ba sau daya ba sau biyu ba in ce zan tashi in je ma ko kuma su mu ce mu su mun gaiyace su, su ki zuwa”
Duk da su na karkashin mulkin soja, Yusuf Tuggar ya ce an yi wa ƙasashen tayin kuɗin tallafin tsaro da kayan aiki don nuna a na tare da su duk da tankiyar da ke tsakani.
Ga kalaman zargi daga Nijar kan Nijeriya da nuna ta na haɗa kai da Faransa don birkita Nijar, Tuggar ya ce zargin na ba wa gwamnatin Nijeriya mamaki kuma bahi da tushe.
Tsohon jakadan Nijeriya a Afurka ta kudu Sulaiman Dahiru ya ce ba farar dabara ba ce ƙasashen uku su dau zaɗin ficewa daga ECOWAS don hakan zai kawo illa ga tattalin arzikin su “ba ruwan su da ECOWAS amma na sha fada daga ƙarshe za su yi nadama duk ƙasashen 3 ba su da iyaka da teku in za su shigo da kaya sai ta Benin, Senegal ko Nijeriya”
Hango maslaha a wanann damɗarwa na da wuya kuma ko bayan saukar shugaba Tinubu a jagorancin shugabannin ECOWAS a watan Yuli mai zuwa da musamman hukumoin Niamey ke ganin ya zama kanwa uwar gami na takunkunmin da su ka dandana bayan kifar da gwamnatin Bazoum.
Kammalawa;
Yanzu dai ga shi ƙasashen na AES sun fice daga ECOWAS bayan ƙarewar wa’adin shekara ɗaya na ƙa’idar yin hakan. ECOWAS a na ta ɗangaren dama ba za ta tilastawa ƙasashen sai lallai sun zauna a ƙungiyar mai ƙasashe 15 ba. A nan ECOWAS har yanzu ba ta kulle ƙofar yin sulhu ba da ba a ƙarin daman a wata 6 nan gaba don ƙasashen su duba ko za su amince su dawo a haɗe da su. ƙarfin ƙasashe masu tasowa na Afurka kan inganta da irin wannan ƙungiyar yanki da kuma uwar ƙungiyoyin wato ƙungiyar AU da ke da babban ofis a Addis Ababa. Duk abun da ’yan Afurka za su yi ba za su zama Turawa don kyalewa ko hulɗa da Faransa ba, ba za su zama Turawa don biyewa Ingila ba. Kazalika ba za su zama Rashawa ba don hulɗa da shugaba Vladimir Putin ba. Idan shugabannin Afurka za su yi aiki don Afirka sannan idan talakawan Afurka za su rayu a matsayin dangin juna to ta nan ne kawai za su iya samun maslaha da sauƙi daga magagin mulkin mallaka.
