Yadda wasu jami’an gwamnati suka bada kwagilar wani asibiti sau biyar

Spread the love

Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (ICPC), Dr. Musa Aliyu (SAN), ya bayyana yadda wani asibiti a Najeriya aka biya kuɗinsa cikakke sau biyar ba tare da an gina shi ba. Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da manyan ‘yan jarida a Abuja, inda ya ce wannan na ɗaya daga cikin misalan yadda cin hanci da rashawa ya yi katutu a ƙasar.

Ya buƙaci ‘yan Najeriya su haɗa kai don yaƙar wannan matsala, yana mai cewa idan ba a daƙile cin hanci ba, ba za a samu ci gaba ba.

Dr. Aliyu ya ƙara da cewa akwai wani ma’aikacin gwamnati da ya saka matarsa, ɗansa da surukinsa a matsayin ma’aikata a jerin sunayen masu karɓar albashi a ma’aikatarsa, duk da cewa ɗansa yana karatu kuma bai kai shekarun yin aiki ba. Haka kuma, ya ce hukumar ta ICPC ta daƙile yunƙurin wawure naira biliyan 20 a bara, wanda da an bar shi, da an sace ƙuɗin.

A cewar shugaban ICPC, akwai kadarori da dukiyoyin Najeriya da na wasu ƙasashen Afirka da aka ɓoye a ƙasashen waje. Ya ce suna aiki tare da hukumomin yaƙi da cin hanci na Afirka don gano waɗannan dukiyoyi da dawo da su gida. Sai dai ya soki ƙasashen da ke ɓoye waɗannan dukiyoyi, yana mai cewa su ne ke taimakawa wajen wawure arzikin Afirka, sannan su na kawo cikas wajen dawo da su.

A karshe, Dr. Aliyu ya buƙaci ‘yan jarida da sauran ‘yan ƙasa su haɗa kai don yaƙar cin hanci da rashawa, yana mai cewa ya kamata a daina girmama da yabo ga mutanen da aka sani da halin rashawa. Ya kuma buƙaci a yi gyara a dokokin ƙasar don tabbatar da cewa duk wanda aka samu da cin hanci ba zai amfana da kuɗin ba, kuma za a hana shi riƙe muƙamin gwamnati har na tsawon shekaru goma.

By ukarofi