Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Jami’an Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin ƙasa Ta’annati (EFCC) a ranar Talata sun kai samame hedikwatar Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) da ke Abuja bisa zargin zamba.
Jami’an waɗanda suka isa ofishin hukumar a cikin wata farar motar bas da misalin ƙarfe 11 na safiyar ranar Talata ɗauke da sahihin sammacin kama wasu ma’aikata, sun bar wurin tare da kakakin hukumar, Fatimah Usara, da wasu ma’aikata uku da har yanzu ba a tantance ko su waye ba.
Majiyoyi sun bayyana cewa kama ta na da nasaba da binciken da ake yi kan almubazzaranci da kuɗaɗe.
Idan ba a manta ba, jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) sun kuma kai samame hedikwatar hukumar bisa zargin karkatar da kuɗaɗen tallafin na Naira biliyan 90 na aikin Hajjin 2024.
Da aka tuntuɓi Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya yi alƙawarin bayar da cikakken bayani idan suka kammala bincike.
