Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Alhaji Abdulƙadir Gambo ɗankoli, ɗaya daga cikin ‘yan takara dake neman shugabancin ƙungiyar masu sayar da maganin ƙwari ta jihar Kano da aka fi sani da Kano State Agro Chemicals Dealers Association, ya ce ya amsa kiran ‘yan ƙungiyar na neman tsayawa takara da niyya da buri na ya ga ya taimaka wajen cigaba da bunƙasa sana’arsu.
Alhaji Abdulƙadir Gambo ɗankoli wanda shi ne Shugaban kamfanin Abdul Adam “ɓenture” kuma shugaban ƙungiyar tsofaffin ɗalibai na Makarantar Sakandire ta Gwammaja “Two” ‘yan aji na 1990 kuma shugaban ƙungiyar cigaban matasa na Lamma ne ya bayyana haka ne da yake zantawa da ‘yan jarida.
Ya bayyana cewa sana’arsu ta sayar da maganin ta daɗe tana fuskantar ƙalubale tsawon lokaci, musamman na rashin ‘yanci da yawan cusgunawa da ake musu daga wasu jami’an tsaro koyaushe suka sayar da kaya ga abokan cinikinsu da suka sayo kaya suka fita dasu daga kasuwa ko kuma idan suka tura yaransu da maganin kwarin zasu kai tashar Mota sai jami’an tsaro su tare su karɓi kuɗi a wajen su alhali ba kayan laifi suke sayarwa ba, yana da nufin kawo ƙarshen irin wannan abu da ake musu.
Alhaji Abdulƙadir ya yi nuni da cewa shi ne ya taɓa bayar da shawara ga magabatansu da suke riƙe da shugabancin ƙungiyar sama da shekaru 30 da ba su wuce mutum 10 ba, da daci da babu suna yi mata hidima saboda ba a taɓa yin zaɓen shugabanni ba tun kafata ya bada shawarar a zo a yi mata tsarin shugabanci na zaɓe da karɓa-karɓa na shugabanci a ka amince da haka aka tara jama’a a wani taro da aka taɓa yi a sansanin yan yawon buɗe ido aka fitar da shugabanci na riƙon kwarya ƙarƙashin jagorancin Alhaji Bello Waziri da mataimakansa da sakatare da Ma’aji da jami’in hulɗa da jama’a ake ta tafiya har aka zo aka fitar da kwamitin dattawan ƙarƙashin shugabancin Alhaji Bala Larabawa da su ake zama taro da ake gudanar na ƙungiyar.
Ya ce a ƙarƙashin shugabancin na riƙo an sami nasarori masu tarin yawa da suka haɗa da yi wa ƙungiyar rijista ta CAC aka samar mata lauya da buɗe dandali a manhajar Whatsapp da ake tuntuɓar juna akan lokaci akan abinda ya shafi cigaban ƙungiya ko akasin haka. Kwamitin riƙon da yanzu kusan shekaru biyu kenan yake gudanar shugabanci har zuwa yanzu da ake shirin gudanar da zaɓe don samar da zaɓaɓɓun shugabannin da za su cigaba da gudanar da ƙungiyar.
Alhaji Abdulƙadir Gambo Dankoli ya ce da farko bashi da wani nufi na shiga neman takarar shugabancin ƙungiyar duba da yadda shi ma nauye-nauye da suke a kansa, amma sai al’umma suka matsa lallai ya fito watakila akwai abinda suka hanga don haka ya baiwa Allah zaɓi ya amsa ya fito wannan takara na neman zama shugaban ƙungiyar na masu sayar da magungunan ƙwari wato Kano State Agrochemical Dealers Association.
Ya ƙara da cewa suna faɗan irin ƙudurinsu da tsare-tsare da za su zo da su da suka ƙunshi haɗa hannu da masu sana’ar maganin ƙwarin don su kai ga nasara na cigaba da bunƙasa sana’arsu da maganta wasu matsaloli da suke fuskanta a ɓangarori da dama da suka dame su.
Alhaji Abdulƙadir Gambo ɗankoli ya ce akwai kamfanoni da ake da su na magungunan kwari sama da 30 a ƙasar nan kuma jihar Kano ce take tallata kayansu, sune abokan kasuwancinsu da tura su duk inda za su je a ciki da wajen ƙasar nan amma suna fuskantar matsaloli tsakanin su da kamfanonin wannan na ɗaya daga abinda suke so su kawo gyara akai da za a kyautata alaƙa tsakaninsu ta nemawa ‘yan ƙungiyar hakkokinsu idan ya zama shugaban ƙungiyar da yardar Allah.
