Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Manyan jiragen dakon mai guda biyu cike maƙil da man jiragen sama kimanin lita miliyan 130 matatar man Dangote ta fitar da daga Nijeriya zuwa ƙasar Saudiyya.
Dangane da hasashen da ƙungiyar ƙasashe Masu Arzikin Man Fetur ta OPEC ta yi na cewa matatar mai ƙarfin tace gangan 650,000 a kowace rana za ta warware matsala a kasuwannin ɗanyen mai da kayyayakin mai a duniya, shugaban rukunin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana sabon shirin fitar da man fetur a matsayin cimma muradun da ƙungiyar ta sanya a gaba.
Haka kuma ci gaban na iya nuna cewa Nijeriya za ta ba yankin gabas ta tsakiya fifiko a burinta na zama cibiyar tace matatun mai a daidai lokacin da ake rufe matatun mai a arewacin duniya.
A watan Disambar da ya gabata, Kamfanin Mai na Nijeriya (NNPCL) ya bayyana cewa ya sayar da kayyakin farko na Port Harcourt Low Sulfur Straight Run oil (LSSR) ga Gulf Transport and Trading Limited (GTT) na Dubai. An ba da rahoton cewa kamfanin ya yi lodi a cikin jirgin ruwan Wonder Star MR1.
Dangote, a wata sanarwa da ya fitar bayan ziyarar da tawagar ƙungiyar Tattalin Arzikin Kasa ta Nijeriya (NESG) ta kai wa kamfanonin Dangote taƙin zamani da kuma matatar man fetur da man fetur da ke Ibeju Lekki, Legas, ya ce abin da matatar ta samu ya kai 550,000.
