Ba zan ba Ribaɗu haƙuri ba – Naja’atu

Spread the love

Daga MUHAMMAD MUJITABA a Kano

Fittaciyar ‘yar gwagwarmayan nan kuma ‘yar siyasa, ‘yar asalin jihar Kano, Hajiya Naja’atu Muhammad, ta bayyana cewa babu wani dalili da zai sa ta janye maganar da ta yi akan gazawar Malam Nuhu Ribaɗo da wannan gwamnatin ta Bola Tinubu ballantana ta ba shi haƙuri kan maganganun da ta yi a wannan lokaci kamar yadda shi Malam Nuhu Ribaɗo mai bawa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro ya nemi ta janye kalamanta kuma ta ba shi haƙuri.

Naja’atu ta bayyana haka ne a wata hira da ta yi da wata kafar yaɗa labarai a birnin Kano a ranar Talatar nan da ta gabata.

Haka kuma ta ƙara da cewa abin da ba gaskiya ba ne in ka faɗa kake janyewa ko ka bada haƙuri amma ita gaskiya ta faɗa don haka ba za ta janye ba kuma ba za ta bada haƙuri ba, kuma ta shirya tsaf domin Malam Nuhu Ribaɗo ya kaita Kotun ƙoli amma tana nan daram akan maganar ta, inda ta ce shi kansa Nuhu Ribaɗo lokacin yana shugaban hukumar yaƙi da taannati da yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya EFCC, ya taɓa bayyana Bola Ahmad Tinubu a matsayin gwamna cikin gwamnonin Nijeriya na kan gaba wajen cin hanci da rashawa a Nijeriya, inda kuma ta ce duk mai kokwanton wannan magana ko shakku akan maganar da Nuhu Ribaɗo ya yi to ya shiga kafar sadarwa ta YouTube don gasganta wannan labari da Malam Nuhu Ribaɗo ya faɗa kan Tinubu.

A ƙarshe wakilinmu ya rawaito mana cewa ita dai Hajiya Naja’atu ‘yar siyasa ce domin kuwa ta taɓa zama Sanata ta Kano ta Tsakiya a wani lokaci da ba a daɗe ba aka samu canjin gwamnati kuma ‘yar gwagwarmaya ce matar ɗan gwagwarmaya Maragayi Dakta Bala Muhammad mai bawa tsohon gwamnan Kano Malam Abubakar Rimi shawara akan harkar siyasa.

Dakta Bala dai an masa kisan gilla ne a wani lokaci da ya gabata kuma a wata hira da aka taɓa yi da Hajiya Naja’atu a wani gidan rediyon a shekarar 1988 ta faɗa cewa bata ga wani amfani na tsoron faɗar gaskiya ba domin kuwa matsorata da yawa sun mutu akan gadon su.

By ukarofi