Babu wata jami’iyya da ta kai APC cancanta, inji Masari

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Aminu Masari, ya ce babu wata jami’iyya madadin gwamnatin APC wajen ceto ’yan Nijeriya.

Masari bayyana haka ne a ranar Lahadi a garin Kafur, ƙaramar Hukumar Kafur, a wajen ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen aananan hukumomin jihar da aka shirya gudanarwa a ranar 15 ga watan Fabrairu.

“Labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta na zamani cewa wasu ‘yan siyasa suna haɗa kai don haɗaka ba komai ba ne illa sake tattaro waɗanda suka rasa tagomashin siyasa a jam’iyyar APC, ta fuskar samun muƙami.

“ƙoƙarin da suka yi na ƙulla ƙawance ba zai kawar da hankalin jam’iyyar APC daga tunani da aiwatar da shirye-shiryen da za su iya rage raɗaɗin talaka ba” tsohon gwamnan jihar Katsina ya bayyana.

Masari ya buƙaci ’yan Nijeriya da su ƙara haƙuri da gwamnatin APC, inda ya ƙara da cewa taɓarɓarewar tattalin arziki da ‘yan Nijeriya ke fuskanta wani lamari ne da ya zama ruwan dare gama duniya.

Ya ci gaba da cewa, a matsayinsa na wanda ya kafa jam’iyyar APC, zai ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da manufofin jam’iyyar.

Masari ya ƙara da cewa, “Ina APC a yau, gobe da kuma kodayaushe saboda ba na cikin jam’iyyar don wani muƙami na siyasa ko naɗi.

Tsohon kakakin ya buƙaci dukkan masu biyayya ga jam’iyyar APC da su yaɗa kyawawan ayyuka da manufofin jam’iyyar tare da roƙon jama’a da su ɗauki duk wani gazawa a matsayin kuskuren ɗan Adam.

“Ina kira ga al’ummar ƙaramar hukumar Kafur da su fito kwansu da kwarkwata domin kada kuri’a ga jam’iyyar APC a zaɓen ƙananan hukumomi mai zuwa,” inji Masari.

Da yake jawabi a wajen taron, babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa Bola Tinubu kan harkokin siyasa, Ibrahim Kabir-Masari, ya buƙaci ‘ya’yan jam’iyyar APC a dukkanin bangarori da su hada kai da juna domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a kodayaushe.

Ya bayyana cewa Tinubu ya bayar da kwangilar sake gina hanyar Zaria zuwa Malumfashi da Funtuwa zuwa Yashe, a ƙoƙarinsa na sauƙaƙa harkokin zamantakewa da tattalin arziki.

Ya kuma ce shugaban ƙasar ya amince da kafa kwalejin koyon aikin gona ta tarayya a Nabanje, Masari.

By ukarofi