
Daga BELLO A. BABAJI
Rundunar ƴan sanda a Jihar Neja ta kama wani Lukman Aliyu mai shekaru 20 bisa zargin lalata da wata ƴar shekara shida a lokacin da ta ke komawa gida daga makaranta.
Haka kuma, ta kama wani mai suna Genesis Yaryok Sunday bisa yin garkuwa da wani ɗan shekara 6 a yankin Sabon-Wuse dake Ƙaramar Hukumar Tafa a jihar.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Minna, ranar Juma’a.
Ya ce rundunar ta kuma yi nasarar kama wasu mutane takwas bisa aikata manyan laifuka da suka haɗa da fashi da makami da ƙwacen waya.
Jami’in ya ce an shigar da ƙarar Lukman Aliyu ne a ranar 30 ga watan Junairu biyo bayan fyaɗe da aka yi wa yarinyar kwana ɗaya kafin nan, wadda aka ga jini na fita daga jikinta.
Tuni aka kama Aliyu a matsayin wanda ake zargi da aikata laifin inda kuma na take ya amsa laifinsa da cewa a wani juji dake kusa da hanyar komawarta gida ya mata fyaɗen.
A halin yanzu dai yarinyar tana Babban Asibitin Nasko a inda ake kula da lafiyarta.
Shi kuwa GY Sunday, wanda maƙoci ne ga yaron, an kama shi ne bayan gano yaron da ya ɓata, a yankin Jere na Jihar Kaduna.
A ranar 29 ga Junairu ne yaron ya ɓata a yankin Sabon-Wuse dake Tafa, inda bayan kama Sunday ne, sai ya amsa cewa shi ne wanda ya yi garkuwa da yaron tare da kai shi unguwar Idah dake Kaduna Road.
Ya yi garkuwa da yaron ne da nufin karɓar N200,000 daga mahaifiyar yaron.
