Allah ba ya ɗaukaka bawansa jahili!

Spread the love

Shi jahilci ciwo ne mai matuƙar illa ga mutum da kuma al’umma baki ɗaya. Shi a ƙashin kansa jahili kan cutu sakamakon jahilcin da ya ke da shi, sannan kuma ayyukansa kan cutar da al’umma sakamakon ko yi da wasu za su yi da ayyukansa a rashin sani. 

Ya zo cikin hadisi daga Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ke cewa; “shugaba ja’iri, da malami kangararre, da kuma mai ƙoƙari (a addini amma) jahili.”

Saboda haka kuwa jahili ba zai taɓa samun ɗaukaka wajen mutane ba, ballantana wajen Allah (S. W.A). 

Shi kuwa haƙuri ɗaukaka ma’abocinsa ya ke yi, domin ta hanyarsa ne ake samun nasarar komai na rayuwa. Saboda haka babu wani mutum da zai kasance mai haƙuri face Allah ya ɗaukaka shi.

Ya zo cikin Usulul-Khafiy daga iddati daga Barƙee, daga Aliyu Bn Hafsi al-ƙurashiy al-Kuufeey zuwa kan Abu Abdullah (aminci ya tabbata a gare shi) ya ce; Allah bai taɓa ɗaukaka (mutum) da jahilci ba, kuma bai taɓa ƙasƙantar (da mutum) ta hanyar haƙuri ba .”

Saboda haka mu ƙara haƙuri cikin komai namu,  kada suka ko zargi ko aibantawa ko kuma cutarwa ya zame mana jarrabawa mafi girma wacce za ta hana mu juriya har ya zama mun yi hasarar duniya da lahirarmu.

Haƙuri siffa ce ta Annabawa (A. S), duk wanda ya yi haƙuri zai sami ɗaukaka daga Allah kamar yadda ya ɗaukaka Annabawansa (A. S).

Wasiƙa daga FATIMA MA’ASUMA. 09070905293 (tes kawai).

By ukarofi