UNICEF ta nuna damuwa kan ƙaruwar cutar shan’inna a Jihar Kano

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Hukumar kula da yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ta nuna matukar damuwa kan ƙaruwar cutar shan inna a Jihar Kano. Shugaban ofishin UNICEF na Kano, Rahma Farah, ya bayyana hakan yayin taron wayar da kai ga shugabannin ƙananan hukumomi 44 da sarakunan gargajiya kan yaƙi da cutar shan inna, allurar rigakafi, da kuma inganta ayyukan kiwon lafiya a matakin farko. Ya ce fiye da rabin miliyan na yara a Kano ba su taɓa samun allurar rigakafi ba, lamarin da ya sa jihar ta zama mafi mai yawan yaran da ba su samu allura ba a Najeriya.

Farah ya ƙara da cewa cutar shan inna tana ƙara yawaita a Kano, inda aka samu rahoton sabbin wanda suka kamu su shida a 2022, 27 a 2023, sai kuma 29 a 2024. Ya ce wannan ƙaruwar mai tayar da hankali na nuni da cewa akwai buƙatar haɗin gwiwa domin kare lafiyar yara daga cututtukan da za a iya kaucewa da allurar rigakafi. Don haka, ya buƙaci shugabannin ƙananan hukumomi, sarakunan gargajiya, da gwamnatin jihar su ƙara ƙaimi wajen gudanar da shirin allurar rigakafi da kuma kafa kwamitocin sa ido masu ƙarfi a kowace ƙaramar hukuma.

Kwamishinan lafiya na Kano, Dr Abubakar Labaran, ya jaddada aniyar gwamnati wajen inganta kiwon lafiya, musamman ɓangaren rigakafi da yaƙi da cutar shan inna. Haka nan, darakta janar na hukumar kula da lafiyar matakin farko ta Jihar Kano, Dr Nasiru Mahmud, ya bayyana cewa taron ya shirya ne domin sabunta bayanai ga masu ruwa da tsaki kan rigakafi da kuma matsalar yaran da ba su samu allura ba. Shugaban kungiyar ALGON na Kano, Jamilu Ɗanbatta, ya sha alwashin haɗa kai da UNICEF domin daƙile cutar shan inna tare da inganta rigakafi a faɗin jihar.

By ukarofi