Rundunar sojin sama ta tabbatar da kuskuren harin dakarunta a Katsina da fara bincike

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rundunar sojin sama (NAF) ta magantu game da iftila’in da ya shafi fararen hula a yankin dutsen Yauni dake ƙauyen Zakka a ƙaramar hukumar Safana ta Jihar Katsina, a ranar Asabar.

Harin, wanda jami’anta suka nufi kai wa ƴan ta’adda, ya yi sanadiyyar kashe mutane shida ƴan gida ɗaya da wani mutum ɗaya.

A wata sanarwa da Daraktan Labaranta, Olusola Akinboyewa ya fitar, Shugaban rundunar, AM Hasan Abubakar, ya umarci a yi bincike mai zurfi game da al’amarin.

Akinboyewa ya ce, dakarun sun gudanar da harin ne musamman don mayar da martani ga ƴan bindigar da suka farmaki ƴan sandan ‘mobile force’ da wasu jami’an sintiri na Community Watch Corps a jihar.

Ya ce, samun rahoton sirri da ke cewa ƴan bindigar sun farmaki jami’an da kashe ƴan sanda biyu da ƴan banga huɗu ya sanya sojojin kai ɗauki.

A cewarsa, sun tabbatar da cewa ƴan bindigar sun samu mafaka a yankin dutsen Yauni.

Ya ƙara da cewa, NAF tana cigaba da ƙoƙarin bin diddigin al’amarin tare da gano gaskiyar abin da ya faru na rasa fararen hular.

Lamarin ya janyo cecekuce da zarge-zarge da ke nuna cewa akwai wata maƙarƙashiya, inda shugaban dakarun ya umarci a zurfafa bincike, ya na mai tabbatar wa al’umma cewa suna ƙoƙarin kare su da dukiyoyinsu.

By Babaji