Abin fashewa ya yi sanadin mutuwar mutum biyu a wata kasuwa a Zamfara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mutane biyu ne suka rasa rayukansu a yayin da wata hodar bindiga ta tarwatse a wata kasuwar ƙauye dake ƙaramar hukumar Talata-Mafara a jihar Zamfara.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata, wanda ya jafe ƴan tireda da masu shaguna cikin firgici tare da guje-guje domin neman tsira.

Wani mutum ya shaida wa manema labarai cewa abin fashewar ya tarwatse ne a wani shago da ake harkar bindigun gargajiya.

Ciyaman ɗin ƙaramar hukumar, Yahaya Yari ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce tuni aka garzaya da waɗanda suka samu raunuka zuwa Asibitin Koyarwa na Usman Ɗan-Fodiyo a Sakkwato don ba su kulawa.

“Aƙalla mutane 44 ne suka jikkata a yayin da abin ya tarwatse”, inji Yari.

Jihar Zamfara dai jiha ce da ke fama da matsanancin rashin tsaro sakamakon tasirin ayyukan ƴan bindiga da garkuwa da mutane.

Ana haɗa bindigun gargajiya ne domin amfanin ƴan banga da ƴan sa kai, lamarin da ke neman zama barazana ga zaman lafiyar al’umma.

By Babaji