Gwamnatin Katsina ta ware Naira biliyan 2.3 don ciyarwa a Ramadan

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kwamishinan Noma na jihar, Farfesa Ahmed Muhammad Bakori ya faɗa wa manema labarai haka bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dikko Raɗɗa.

Ya ce kuɗin da gwamnatin ta ware za ta sayi nau’ukan hatsi da suka haɗa da shinkafa da masara domin raba wa marasa ƙarfi da masu nisan shekaru kyauta a lokacin azumin watan Ramadan.

Bakori ya ƙara da cewa gwamnati tana gudanar da wannan shiri a kowacce shekara domin sauƙaƙa wa al’ummar musulmi su gudanar da ibadu cikin nitsuwa.

“Za a raba kayan abincin gida biyu; Kashi guda a raba wa mabuƙata kyauta, sauran kuma a sayar wa al’umma bisa farashi mai rangwame”, inji kwamishinan.

Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnati ta ware Naira biliyan 16.5 domin sayo ton 32,000 na takin zamani domin raba wa manoma a watan Afrilu mai zuwa.

Ya ce dama akwai buhu 80,000 a ajiye, waɗanda za a haɗa sai a raba wa manoma a damina mai zuwa.

By Babaji