Yanzu-yanzu: Shugaban sojojin ƙasa ya je Zamfara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Jagoran sojojin ƙasa (COAS) Laftanal Janar Olufemi Oluyede yana Gusau, babban birnin jihar Zamfara a halin yanzu, a wata ziyara ta kwana ɗaya.

A yayin ziyarar ne zai gana da tawagar atisayen ‘Fansan Yamma’, ƙarƙarshin jagorancin shugabanta, wato Manjo-Janar Oluyinka Soyele.

Blueprint ta ruwaito cewa, babban jami’in zai kuma ziyarci hedikwatar Birget ta ɗaya ta rundunar dake Gusau da rukunin ‘Garrison Cantonment’, inda zai gabatar da jawabi ga dakarun.

Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da matsanancin rashin tsaro sakamakon ayyukan ƴan bindiga tsawon sama da shekaru goma.

By Babaji