Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Babban limamin masallacin Juma’a na Hidaya da ke Kundila Gandun Albasa, Sheikh Kamalu Inuwa, ya bayyana cewa duk shugaban da ya hau karagar mulki a kowane mataki na shugabanci ya yi kama karya ya taka mutane ko tursasa musu ya yi abin da ya ga dama na zaluntar al’umma da ke ƙarƙashinsa, to sai Allah ya ƙaskantar da shi a idon al’ummar da ya zalunta bayan Allah ya ƙwace mulkin daga hannusa kamar yadda duk wani shugaba da ya yi adalci sai ya samu soyayya, girma da daraja.
Saboda haka, Sarkin Malaman ya shawarci duk wani shugaba da aka rantsar, ya ɗau takardar rantsuwar sa ya ajiye a ƙarƙashin filon da yake kwanciya kullum, ya dinga duba ta kan alƙawarin da ya yi a cikin rantsuwar domin ta zame masa linzami wajen tafi da mulkinsa lami lafiya da adalci domin ya yi kyakkyawan ƙarshe da sauransu daga al’umma.
Sarkin Malaman ya faɗi haka ne a cikin fassarar huɗubarsa da ya yi akan yaƙar zuciya ta yi abun kirki ta bar akasin sa wanda yaƙi da zuciya shi ne babban rabo da mutum zai samu a wannan duniya da lahira baki ɗaya a nasihar Sarkin Malamai Babban limamin masallacin Juma’a na Hidaya da ke Kwandila Kano.
Dangane da nasiha akan yaƙar zuciya don mutum ya zama a tafarki madaidaici ya ce abu ne abu biyu akwai wanda bawan zuciya ne sai abin da zuciya ta ke so zai yi akwai wanda ya mallaki zuciya shi ne mai yaƙar zuciya ya fi ƙarfin ta domin a aikata abin da Allah yake so da barin abin da Allah baya so mai haka shi ne ya yaƙi zuciyarsa shi ne mai rabo a duniya da lahira kamar yadda bayanai suka zo a ayoyi masu yawa a littafin Allah mai girma yace akwai hanyoyi da dama da zai gane matsayinsa yaya zuciyarsa ta ke shi ne kullum ya riƙa yi wa kansa hisabi ta hanyar tambayar kansa yau sallah nawa ya samu a jam’i ina ya je zumunci wa ya taimaka a yan uwansa da maƙotansa wane ya ma masallaci ko makaranta ko Islamiyya a unguwarsu da sauransu wannan kuma bawai sai mai tarin kuɗi da ake ganin shi ne mai kuɗi ba ko wa ya yi gwargwadon ikonsa.
A ƙarshe Sheikh Kamalu Inuwa Sarkin Malamai ya yi nasiha ga ‘yan kasuwa kan su ji tsoran Allah a dukkan al’amuransu na kasuwanci ta hanyar siyowa da sauƙii su siyar da sauƙi domin samun albarkar kasuwancinsu musamman da muke cikin ƙarshen Sha’aban na cewa Ramadan watan azumin Musulmin duniya na zuwa to akwai buƙatar a sauƙaƙa a taimakawa mutane raunana Dan Allah a guji nuna mabuƙata a faifan ɓidiyo da kafafan yaɗa labarai domin wani duk buƙatarsa bazai so a nuna shi a duniya ba don haka a yi don Allah ko da za a faɗa don wani ya yi koyi to ba sai an nuna hotuna ko fuskokin su ana basu taimako ba in kayi dan Allah to yafi ka sani abin da zai sakama don haka a nemi yardar Allah ba neman yardar mutane ba shehu malamin dai yayi bayani mai tsawo akan tarihin zahararrun masu mulki kamar su ƙaruna da sauransu in da kuma ya ja hankali alumma da kowa ya guji aikata ba dai dai ba domin yin dai dai wanda ya dace da kyakyawar tarbiyyar soron Allah domin kyakyawan ƙarshen duniya da lahira.
