Yadda Real Madrid ta fitar da Man City daga gasar Zakarun Turai

Spread the love

Real Madrid ta fitar da Manchester City a wasan cike gurbi a Gasar Zakarun Turai, bayan da ta ci 3-1 ranar Laraba a Santiago Bernabeu.

Real Madrid ta kai zagayen gaba da cin 6-3 gida da waje kenan, bayan da ta yi nasara 3-2 a Etihad ranar Talata 11 ga watan Fabrairu.

City ta ci ƙwallo biyu ta hannun Erling Haaland a Etihad, yayin da Kylian Mbappe da Brahim Diaz da Jude Bellingham suka ci wa Real Madrid ƙwallayenta.

Kylian Mbappe ne ya fara cin ƙwallo a minti na 4 da fara wasan, karon farko da Real ta ci ƙwallo da wuri a Champions League tun bayan Afirilun 2018 a wasa da Juventus da ta zura ƙwallo a minti 2:47.

Kuma shi ne karon farko da aka ci City ƙwallo a cikin ƙanƙanin lokaci a gasar ta zakarun Turai tun bayan Oktoban 2018 a wasa da Hoffenheim da aka zura mata ƙwallo a 00:43.

Haka kuma ƙyaftin ɗin Faransa, shi ne ya zura na biyu da na uku, kenan ya zura uku rigis a ragar City, inda ay ci ƙwallaye 28 ke nan a dukkan fafatawa a Real Madrid a kakar nan.

Babu ɗan wasan da ya zura ƙwallaye da yawa a raga a irin wannan zagayen a Champions League a tarihi fiye da Mbappe mai 23.

Mbappe mai shekara 26 da kwana 61 yana da hannu a cin ƙwallo 500 a dukkan karawa tsakanin ƙungiya da Faransa, wanda ya ci 358 ya bayar da 142 aka zura a raga.

Daf da za a tashi daga wasan Man City ta zare ɗaya ta hannun Nico Gonzalez.

Real Madrid ce mai riƙe da kofin zakarun Turai na 15 jimilla, ita kuwa City tana da ɗaya tal.

Wannan shi ne karo na 14 da suka fuskanci juna a Champions League, inda Real ta yi nasara biyar da canjaras biyar, Man City kuma ta ci huɗu daga ciki.

Wannan shi ne karo na 10 da Carlo Ancelotti da Pep Guardiola suka fuskanci juna a Champions League, yayin da wasa takwas daga ciki an yi ne tsakanin Real Madrid da Manchester City.

ƙungiyoyin da suka fara kai wa zagaye na biyu kai tsaye a kakar bana da aka sauya fasali a Champions League sun haɗa da Arsenal da Aston Villa.

Sauran sun haɗa da Atletico Madrid da Barcelona da Inter Milan da Leverkusen da Lille da kuma Liverpool.

Ranar Juma’a 21 ga watan Fabrairu za a raba jadawalin ƙungiyoyi 16 – za kuma a fara wasannin zagaye na biyu daga makon farko na watan Maris.

By ukarofi