Daga UNCLE LARABI
Tabbas muna da rawar da za mu taka wajen daƙile hana ƙarin kuɗin kiran waya da kuɗin data tunda iyakar talaka kawai zai fi ba wa illa. Amma da yake mu lusarai ne, mun miƙe ƙafa muna jiran a turo mana mala’iku daga sama su ƙwatar mana ‘yanci. Lusarancinmu ba zai bar mu mu taka rawar ba har mu kai ga gaci ba.
Ba sai an ɗauki makami ko an fasa kayan gwamnati da na al’umma kaɗai shine hanyar cimma buri ko kawar da zalunci ba, alƙalami yana da matuƙar tasiri sosai wajen kawar da zalunci har gobe. Sannan akwai wasu hanyoyin da za a bi cikin ruwan sanyi sai ka ga ruwan randa ya dafa ganda.
Misali; hanyar da za mu kawar da wannan zaluncin shine mu ɗauki tashon kwana guda kar wanda ya yi kiran waya ko saƙon tes ko ya buɗe data ɗinsa, don gudanar da wani uzuri a ‘social media’.
Hakan zai haifar wa kamfanonin sadarwa da gwamnati matuƙar asarar da za su ji a jikinsu su janye ƙudirinsu.
Na san wasu za su ce ba za su iya hakan ba. To, da yawan waɗanda za su faɗi haka ba su rayu a shekarun 70’s da 80’s da 90’s ba, lokacin da babu wayar ma gabaɗayanta sai ‘land line’ ko ta ‘pay phone café’. Shi ma a ƙarshen 90’s zuwa farkon 2000 suka ɗan yi tasiri sosai, daga baya sai wayar hannu ta ‘cellular’ da ‘GSM’ suka bayyana har mu ke rayuwa da su a yanzu muke ganin ba za mu iya ɗauke numfashi a kansu ba na tsahon kwana guda, wato ‘24 hours’ ba.
Ina ma za mu daure mugu hakan da za mu fara gwada wa kanmu ƙwatar ’yanci ta hanyar irin kalar namu lalacin ga azzaluman da ba su da niyyar sauƙaƙa wa talakawan ƙasarmu Nijeriya.
Amma muddin muka ce haka za mu cigaba da zama muna miƙe ƙafa tare da jingina komai daga Allah ne ko Allah ya hore mana ya ba mu abin siya, to, tabbas ba mu shirya ganin ƙarshen wannan rayuwar ta zalunci ga azzaluman shugabannin da suke sace dukiyar ƙasarmu suna azurta kansu da bar wa iyalansu dukiyar da ba za ta amfane su ba.
Idan mun ahirya neman gyara da ƙwatar ’yancinmu ta sassaukar hanya, to, ya kamata mu shirya rana da lokacin da za mu ƙaurawace wa kiran waya da buɗe data.
ƙarshe: Idan mun ce ba za mu iya ba, kamfanonin da kansu sun sha haramta mana kiran waya da data har na tsawon kwanaki ta hanyar ‘up grade’ ko ‘network problems’.
Uncle Larabi (Abdullahi Jibril Dankantoma) ya rubuto ne daga Jihar Kano – Nigeria. Za a iya samun sa a 08065418892. Juma’a, 14 ga Fabrairu, 2025
