Sojoji sun kama ɓarayin mai 17 da tarwatsa wajen ajiyarsu 18

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Dakarun Runduna ta 6 ta sojojin Nijeriya da ke aiki tare da wasu hukumomin tsaro, sun yi nasarar daƙile ayyukan wasu ɓata-gari a Kudancin ƙasar.

A atisayen da suka gudanar daga ranar 17 zuwa 23 ga watan Fabrairu, 2025, jami’an sun tarwatsa haramtattun wajen tace ɗanyen mai guda 18 da kama mutane 17 da ake zargi da hannu a aikata laifukan satar mai.

Sun kuma kame jiragen ruwa 10 da ake gudanar da ayyukan da su gami da kama lita 25,000 da aka sace a yankin Neja-Delta.

A ranar Lahadi ne Mataimakin Daraktan yaɗa labarai na riƙon ƙwarya na rundunar, Laftanal Kanal Ɗanjuma Jona Ɗanjuma, wata sanarwa da ya fitar a Fatakwal, ya ce jami’an sun gudanar da baki ɗaya atisayen ne a Jihar Ribas.

Ya ce, sun tarwatsa haramtattun wajen tace mai guda biyu da kama jiragen katako ɗauke da ɗanyen mai lita 9,000.

Mataimakin Daraktan Labaran ya kuma ce jami’an sun kama wata tirela ɗauke da sama lita 3,000 na ɗanyen man da aka sace.

Haka ma a Jihar Bayelsa, an kama haramtattun wajen tace mai guda uku da na’urar zuƙowa da sama da lita 3,500 na ɗanyen mai da kuma jiragen katako guda biyu da dai sauransu.

By Babaji