
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi (NDLEA), ta kama wata ƴar ƙasar Thailand mai suna Mis Pattaphi Wimonnat a Filin Jiragen sama na Murtala Muhammad dake Legas a lokacin da ta yi yunƙurin shigowa da wasu kayayyaki da suka ƙunshi tabar wiwi.
Matar mai shekaru 24, ta yi dakon kayan ne mai nauyin kilogram 46.60 wadda ta nufi shigowa da shi Nijeriya.
Jami’an NDLEA sun kama ta ne a yayin wani babban atisaye a lokacin da ta yi yunƙurin fasa-ƙaurin kayan.
Daraktan yaɗa labarai na hukumar, Femi Babafemi ya ce an gano tabar ne ƙunshe acikin kayan matar.
A lokacin da ake gudanar da bincike akanta, matar ta ce an ɗauke haya ne a matsayin wadda za ta yi jigilar magani, inda aka yi mata alƙawarin biyanta Dala 3,000 a lokacin da ta yi nasarar kai kayan Nijeriya.
A ranar Alhamis 20, ga watan Fabrairu ne aka kamata bayan ta taho daga Thailand a lokacin da ake tantance fasinjojin Qatar Airways da suka zo daga Doha ta ƙasar Ƙatar.
Har’ilayau, bayan zurfafa bincike game da masu alaƙa da lamarin, jami’an sun kama wani mai suna Samuel Bitris a gidansa dake Ajah a Legas da wasu mutum biyu dake aikin kai saƙo a babur.
A Jihar Nasarawa kuwa, jami’an NDLEA sun kama mutane biyu, wato Bello Adamu mai shekaru 40 da Pius Azuka mai shekaru 42, a yankin ƙananan hukumomi Kokona da Keffi ɗauke da kilogram 517 na taba samfurin ‘skunk’ a ranar 22 ga Fabrairu.
Bugu da ƙari, an kama wasu mutum biyu – Usman Ruwa mai shekaru 43 da Yunusa Haruna mai shekaru 45 a Jihar Neja bisa safarar kilogram 62.7 na skunk a wata mota ƙirar Toyota Corolla a hanyar Sabon Asibiti dake Kontagora a ranar 20 ga watan Fabrairu.
