Rikicin APC a Kano: Minista Ata ba ɗan jam’iyyar APC ba ne, inji Shugaban Jam’iyya

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Jam’iyyar APC mai adawa a jihar Kano ta mayar wa ministan ma’aikatar gidaje na Najeriya, Yusuf Abdullahi Ata da martani kan kalamansa na baya baya nan inda ya yi barazanar ficewa daga jam’iyyar.

Ministan ya yi barazanar ficewa daga APC muddin shugaban jam’iyyar na Kano, Hon Abdullahi Abbas ya sake dawo wa a matsayin shugaban jam’iyyar na jihar a karo na huɗu.

A halin da ake ciki yanzu akwai zafaffan kalaman ministan a wani hoton bidiyo sun karaɗe shafukan sada zumunta, wanda wani abu ne da ke ci gaba da tayar da ƙura a siyasar jihar Kano.

Sai dai shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas ya shaidawa manema labarai cewa Yusuf Ata ‘ba ɗan jam’iyyar bane’ sannan sun yi mamakin dalilan da suka sa aka ɗauko shi har aka ba shi muƙamin minista.

By ukarofi