Zargin Badaƙala: Sunan Yahaya Bello ba ya kan takardar kadarori, inji shaidar EFCC a kotu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Litinin ne Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta ɗage sauraron ƙarar da Hukumar EFCC ta shigar akan toshon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello zuwa ranakun 6 da 7 na watan Maris, 2025.

Hakan na zuwan ne a lokacin da kotun ta nemi EFCC ta gabatar wa kotun shaida, wanda zai bayyana yadda aka samu sunan Yahaya Bello a matsayin wanda ya mallaki wata kadara a wani yanki na Abuja.

Wani mai suna Segun Joseph Adeleke, wanda shaida ne na EFCC kuma Manajan Kamfanin Efab Properties Limited, ya bayyana wa kotun cewa babu sunan tsohon gwamnan acikin takardar sunayen masu kadarori biyu da aka yi bincike akansu.

Daga nan ne kotun ta sake bai wa Lauyan EFCC damar gabatar da wani shaidar game wata kadara dake ‘5th Avenue’ a Gwarimpa.

A nan ma shaidar cewa ya yi wani mai suna Nuhu Mohammed ne ya sayi wannan akan Naira miliyan 70 wanda aka biya ta hanyar tura kuɗin ta asusun banki.

Daga nan, an sake gabatar da wasu shaidu, waɗanda daga cikin kalamansu babu wadda ta danganci Yahaya Bello game da mallakar wata kadara daga cikin waɗanda aka gabatar wa kotun.

Baya ga haka ne Alƙali Emeka Nwite ya ɗage sauraron ƙarar.

By Babaji