Akwai yiwuwar a samu ƙarancin fetur bayan IPMAN ta yi barazanar shiga yajin aiki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ƴan Nijeriya za su iya fuskantar matsalar ƙarancin man fetur a ƴan kwanakin nan sakamakon yunƙurin Ƙungiyar Ƴan kasuwar Fetur ta Ƙasa (IPMAN), na shiga yajin aiki bisa rashin biyan su waɗansu kuɗaɗen ƙa’ida da adadinsu ya kai Naira biliyan 100.

A wani saƙo da Shugaban ƙungiyar, Alhaji Yahaya Alhassan ya fitar a Abuja, ƙungiyar ta ce matuƙar Hukumar tace ɗanyen mai ta Ƙasa (NMDPRA) ta gaza biyan su a lokacin da aka tsara, to ƴan kasuwa za su dakatar da raba fetur ga gidajen mai a faɗin Nijeriya.

Ƙungiyar ta koka ganin yadda sama da shekara ɗaya kenan da aka gabatar mata da buƙatar biyan kuɗin, amma har yanzu NMDPRA ba ta yunƙura ba.

A baya ne dai NMDPRA ta yi alƙawarin biyan kuɗin a yayin taron masu-ruwa-da-tsak a daren sanar da shiga yajin aikin da ƙungiyar NARTO ta yi kan rashin biyan kuɗaɗen.

Ya ƙara da cewa, duk da alwashin da NMDPRA ta ɗauka na cewa za ta biya acikin kwana 40 a gaban Malam Nuhu Ribaɗu (NSA), ba ta cika ba bayan watanni, kuma har yanzu babu tsammanin biya.

By Babaji