Haƙiƙanin abin da ya faru abin takaici ne na yadda har rayuwar ɗalibi ta salwanta. Abin ya samu asali ne yadda ɗan acaba ya ɗauki ɗalibin zai kai shi cikin gari. A hanya JTF suka tsayar da mai mashin ɗin ganin ya yi musu kama da ɗan taadda da ya gudu a hannunsu amma ɗan acabar bai tsaya ba, su kuma suka yi harbi.
Abin takaici harsashin ya shafi ɗalibin FUDMA kuma kafin a isa asibiti rai ya yi halinsa. Shugaban jami’ar FUDMA farfesa Armayau Hamisu Bichi ya tabbatar komai ya nutsa a halin yanzu kuma ya ɗau mataki na gaggawa kan komai ya koma yadda yake sannan za a ɗau dukkan matakin da ya dace don bi wa ɗalibin haƙƙinsa kuma a halin da ake ciki wanda ya aikata wanan laifi tuni yana hannu.
Farfesan ya nuna damuwa ƙwarai da gaske kuma ba zai bar abin ya tafi a haka ba. Tuni jami’an tsaro suna kan batun.
