Ka girmama matata – Mijin Sanata Natasha ga Akpabio

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Mai Martaba Chief Emmanuel Oristejolomi Uduaghan, mijin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ya fito fili ya yi magana kan zargin cin zarafi da matarsa ta yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Uduaghan ya bayyana cewa ya yi ƙoƙarin kauce wa magana kan batun, amma abubuwan da ke faruwa sun sa dole ya bayyana matsayarsa.

Uduaghan ya ce matarsa ta sanar da shi dangantakar da ke tsakaninta da Shugaban Majalisar Dattawa, wanda ya ɗauka a matsayin aboki na iyali. Ya ƙara da cewa Natasha ta samu nasarar lashe zaɓen sanata ne saboda ƙauna da amincewar al’ummarta, kuma ita mace ce mai gaskiya da riƙon amana. Ya buƙaci Majalisar Dattawa da shugaban majalisar su mutunta matarsa tare da ba ta damar yin aikinta ba tare da tsangwama ba.

Sanata Natasha ta zargi Akpabio da toshe mata hanyoyin gabatar da ƙudurorinta da kuma ƙoƙarin razana ta bayan ta ƙi amincewa da wata buƙatarsa.

Lamarin ya ƙara yin ƙamari bayan ta bayyana a wani shirin Arise News inda ta yi ikirarin cewa Akpabio na ƙoƙarin cin mutuncinta. Sai dai matar Akpabio, Unoma, ta musanta zarge-zargen, tana mai cewa dangantakar iyalansu da Natasha ta kasance mai kyau tun kafin ta yi aure.

Lamarin ya ɗauki sabon salo bayan Natasha ta rubutawa Unoma wasiƙa, tana mai cewa zargin da take yi ba ya shafarta, kuma ya kamata ta bar mijinta ya kare kansa. A gefe guda, Unoma ta shigar da ƙara a kotu, inda take neman diyyar naira biliyan 350 daga Natasha bisa zargin ɓata suna da take haƙƙin ɗan Adam. Wannan rikici ya jawo cece-kuce a faɗin ƙasa, yayin da ake jiran matakin da kotu za ta ɗauka.

By ukarofi