Babu rashin jituwa tsakanina da Yari da Matawalle – Hon. Jaji

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Birnin Magaji da ƙaura Namoda, Hon. Aminu Sani Jaji ya ƙaryata raɗe-raɗin cewa ana takun saƙa tsakaninsa da Sanata Abdulaziz Yari da ministan tsaro Bello Muhammad Matawalle. 

Hon. Jaji ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a gidansa da ke Gusau ranar Alhamis. 

A cewarsa, ba shi da wani ra’ayi na ƙashin kansa na nuna rashin jituwa tsakanin shi da Sanata Abdulaziz Yari da Matawalle kamar yadda ake yayatawa a shafukan sada zumunta. 

Hon. Jaji ya bayyana jam’iyyar APC a Zamfara a matsayin tsintsiya maɗaurinki ɗaya, inda ya ƙara da cewa burinsa na tsayawa takarar gwamna a 2027 babu abinda zai tsaida shi. 

“Bani da wata matsala da Sanata Abdulaziz Yari da kuma ministan tsaro Bello Muhammad Matawalle kamar yadda ake yayatawa a shafukan sada zumunta, Hakazalika al’amuran siyasa ta da aka fi sani da Jajiyya Amana a ƙarƙashin jam’iyyar APC yunƙuri ne na ci gaban jam’iyyar don kar a kawo ɓaraka a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar a jihar Zamfara,” ya ce. 

Hon. Aminu Sani Jaji ya jaddada buƙatar haɗin kai tsakanin duk wani ɗan jam’iyyar APC a jihar Zamfara domin samun nasara da ci gabanta. 

A cewarsa, babu wata jam’iyyar siyasa da za ta yi nasara idan babu haɗin kai a tsakanin mambobinta. 

Hon. Jaji wanda ya koka da yadda wasu gungun marasa kishin ƙasa a cikin jam’iyyar APC a jihar ke ƙoƙarin haifar da rikici a jam’iyyar ya kuma bayyana cewa ba za su bari wani mutum ko wasu jama’a su ruguza jam’iyyar ba.

“Mu ne muka gina APC a Zamfara kuma ba za mu bari wani ya riƙa yunƙuri ko kawo rashin haɗin kai a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar a jihar ba,” Hon Jaji ya ƙara da cewa.

By ukarofi