Murnar cika shekara 88: Tinubu ya ayyyana Obasanjo a matsayin rigimamme

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi fatan alheri ga tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, a yayin cikar sa shekaru 88 a duniya, yayin da ya bayyana shi a matsayin “mutum rigimamme ko mai tsauri a wasu lokuta”.

A cikin saƙon da ya fitar a ranar Laraba, 5 ga watan Maris 2025, Tinubu ya bayyana Obasanjo a matsayin gwarzo wanda rayuwarsa na da matuƙar alaƙa da tarihin Nijeriya. 

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ne ya fitar da bayanin shugaban aasar a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Tiwita.

Bola Tinubu ya ce, Obasanjo ya taka muhimmiyar rawa a lokacin da ake buaatar jagoranci mai aarfi, kuma ya sadaukar da rayuwarsa wajen tabbatar da dunƙulewar ƙasa da zaman lafiya.

Tinubu ya faɗi rawar da Obasanjo ya taka yana soja, inda ya kaɓi takardar miƙa wuya daga kwamandan sojin Biyafara, Kanal Philip Effiong, wanda hakan ya kawo ƙarshen yaƙin basasa.

Ya kuma tunatar da yadda Obasanjo ya zama shugaban mulkin soja bayan rasuwar Janar Murtala Mohammed a shekarar 1976.

Bayan haka, Tinubu ya bayyana yadda Obasanjo ya gudanar da zaɓen farar hula tare da miƙa mulki ga gwamnatin dimokuraɗiyya a 1979.

Bayan shekaru 20, a 1999, Obasanjo ya sake dawowa mulki a matsayin shugaban ƙasa na farar hula, ya jagoranci sabuwar dimokuraɗiyya da ke tafiya har zuwa yau.

Tinubu ya bayyana cewa ko da bayan barinsa mulki, Obasanjo na da tasiri sosai a harkokin siyasa da shugabanci, a cikin Nijeriya da kuma ƙasashen duniya.

Ya ce, Obasanjo yana taka muhimmiyar rawa a shawarwari kan zaman lafiya da warware rigingimu a Afirka.

Ko da yake yana da ra’ayoyi na daban a wasu lokuta, Tinubu ya ce hakan yana taimakawa wajen sa ido a kan shugabanci da kuma tsara manufofin gwamnati. 

Shugaba Tinubu ya gode wa tsohon shugaban ƙasa bisa irin gagarumin gudunmuwar da ya bayar ga Nijeriya.

Ya roƙi Allah ya ƙara masa lafiya da tsawon rai domin ƙasar nan da Afirka su ci gaba da amfana da hikima da basirarsa.

Daga ƙarshe, shugaba Tinubu ya miƙa saƙon taya murna ga Obasanjo a madadin gwamnatin Nijeriya da al’umma baki ɗaya, yana mai cewa, “Ina taya wannan babban jigo na Nijeriya murnar cika shekaru 88. Allah ya ƙara maka lafiya da albarka.” 

By ukarofi