Wani coci ya raba wa Musulmi kayan abincin Ramadan a Kaduna

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Cocin Christ Evangelical and Life Intercessory Ministry da ke unguwar Sabon Tasha a ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna ya raba wa Musulmi masu ƙananan ƙarfi da makarantun addinin Musulunci kayan abinci a lokacin azumi.

Shugaban coci, Fasto Yohanna Buru ne ya jagoranci raba kayan abincin, inda ya ce ya yi haka ne domin ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin musulmi da kirista.

“Muna mayar da biki ne kan yadda Hajiya Ramatu Tijjani take yawan ba kirista kayan abinci a lokacin bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara,” inji shi.

Fasto Buru ya ce suna da burin tallafa wa aƙalla mutum 1,000 ne a azumin na bana, sannan ya ce ya jagoranci haɗa malamai da fastoci aƙalla guda 30 domin gangamin jawo hankalin ’yan kasuwa game da muhammancin rage farashin kayan abinci.

Ya ƙara da cewa, “Muna kuma ƙara wa Hajiya Ramatu Tijjani alheri, wata musulma da take ba da tallafin shinkafa, tsabar kuɗi, da sabbin tufafi ga zawarawan cocin da marayu a lokutan bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara da kuma Easter.

A cewar Fasto Buru, cocin ta kwashe shekaru 19 tana rabon shinkafa, masara, da sauran kayan abinci ga al’ummar Musulmi a jihohi biyar na Arewa, wanda hakan ya ba su damar shiga kwarya-kwaryar gudanar da azumin kwanaki 30 da kuma addu’o’in watan Ramadan.

By ukarofi