Komawarka SDP ba zai ɗaga mana hankali ba – APC ga El-Rufa’i

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Jam’iyyar APC a Kaduna, ta nuna halin ko-in-kula game da ficewar tsohon gwamnan jihar, Nasiru El-Rufa’i zuwa SDP, ta na mai cewa hakan bai dame ta ba.

A wani saƙo da aka wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Litinin, El-Rufa’i ya sanar da cewa ya yi murabus daga APC bayan miƙa saƙonsa ga gundumarsa a Kaduna.

Ya zargi shugabancin jam’iyyar da ƙin bi ƙa’idodinta da yin watsi da hanyoyin demokraɗiyya na cikin gida.

El-Rufa’i ya bayyana rashin jituwa da ke cigaba da ƙaruwa a tsakaninsa da alƙiblar jam’iyyar a matsayin dalilinsa na ficewa.

Ya koka ga yadda jam’iyyar ta sauka daga tsari na cigaba da waɗanda suka ƙirƙiro ta suka ɗora ta a kai.

Saidai, a yayin da ya ke tsokaci game da batun, Sakataren APC a Kaduna, Alhaji Yahaya Baba-Pate, ya ce jam’iyyar ba ta damu da ficewar tsohon gwamnan ba, inda ya ce ta mayar da hankali ne wajen cimma nasarar Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Uba Sani a zaɓen 2027.

Ya ce, APC ta na ƙara samun karɓuwa a jihar la’akari da wasu manyan ƴan siyasa da suke shigar ta, wanda ke nuna tana ƙara ƙarfi.

“Ba ma rasa bacci saboda ficewar El-Rufa’i. Jami’yyar a jihar ta yi ƙarfi sama da yadda take a baya”, inji shi.

By Babaji