Shettima, Wike, Fubara da wasu gwamnoni sun gana da Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa

Spread the love

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima, tare da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, da gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, sun halarci liyafar buɗa baki tare da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a daren Litinin. Haka kuma wasu gwamnoni daga jihohi daban-daban sun kasance a wurin, ciki har da Alex Otti na Abia, Umo Eno na Akwa Ibom, Bala Mohammed na Bauchi, Hyacinth Alia na Benue, Babagana Zulum na Borno, Sheriff Oborevwori na Delta, da Muhammad Yahaya na Gombe.

Baya ga gwamnonin, shugabannin hukumomi da dama suma sun halarta, ciki har da shugaban hukumar kula da aikin hajji ta ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Mukhtar Muhammad; Muƙaddashin shugaban hukumar gyaran hali (NCS), Sylvester Ndidi Nwakuche; shugaban hukumar kula da gobara (FFS), Jaji Abdulganiyu; da shugaban hukumar kwastam ta ƙasa (NCS), Bashir Adeniyi.

An gudanar da wannan liyafa ne domin ci gaba da kyautata alaƙa da tuntuɓar juna tsakanin shugabannin gwamnati, yayin da Shugaba Tinubu ke kira ga shugabanni da su mayar da hankali wajen taimakon talakawa da kuma marasa galihu a faɗin kasar.

By ukarofi