Makarantar marayu ta Shettima na inganta rayuwa a Maiduguri

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

A Kumshe, yankin Lamisula a Maiduguri, Jihar Borno, wata sabuwar makarantar marayu mai suna KSM Academy ta fara aiki, tana ba da ilimi kyauta ga yara marayu da suka rasa iyayensu sakamakon rikicin Boko Haram. Makarantar, wadda ita ce irin ta farko a yankin, ta ƙunshi manyan gine-ginen ajujuwa na bene hawa biyu tare da kayan karatu na zamani. An kuma ƙawata ganuwar makarantar da zanuka masu ƙayatarwa don samar da yanayi mai annashuwa ga yara.

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya ƙirƙiro wannan makaranta, ya bayyana cewa burinsa shi ne bai wa yaran da suka rasa iyayensu damar samun ilimi mai inganci da kuma tarbiyya.

Ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da wakilan Rotary International a Fadar shugaban ƙasa, inda ya jaddada cewa ilimi shi ne hanya mafi dacewa don canza rayuwar marasa galihu da kuma bunƙasa Najeriya gaba ɗaya.

A cewar Shettima, makarantar ba kawai wurin karatu ba ce, har ila yau, tana ba da abinci kyauta ga ɗalibai don rage nauyin iyalai da kuma tabbatar da ci gaba da halartar makaranta.

Bugu da ƙari, ana gudanar da shirye shiryen tallafin ƙwaƙwalwa da jin daɗin yara marayu domin rage raɗaɗin abubuwan da suka faru da su a baya. Haka kuma, makarantar na da tsarin koyar da ilimi da ke inganta tunanin yara tare da basu damar zama jagorori na gari a nan gaba.

Mataimakin shugaban ƙasa ya yi kira ga sauran shugabanni da masu hannu da shuni da su yi koyi da irin wannan tsari wajen samar da ilimi kyauta ga yara musamman a yankunan da rikice-rikice suka shafa. Ya ce ɗaukar matakin samar da ilimi kyauta ga yara zai taimaka wajen rage jahilci da talauci tare da bunƙasa zaman lafiya a Najeriya.

Ɗaliban makarantar, waɗanda ke sanye da kayan makaranta masu kyau, suna nuna farin ciki da jin daɗin kasancewarsu a wannan muhalli na ilimi.

Wata ɗaliba mai suna Zainab ta bayyana cewa “Na ji daɗi sosai da samun wannan dama, yanzu zan iya yin burina na zama likita.” Wannan yana nuna irin tasirin da wannan shiri ke da shi wajen canza rayuwar yara marayu a yankin Arewa maso Gabas.

By ukarofi