NELFUND: Gwamnatin Tarayya ta bai wa ɗalibai a Arewa rancen biliyan N12.28

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Domin biyan kuɗin karatu ga ɗaliban Arewacin ƙasar nan guda 133,328, Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ƙarƙashin shirin ta na bada lamunin karatu ga ɗalibai (NELFUND) ta biya kuɗi har Naira biliyan 12.28.

Jihar Borno dake Arewa maso Gabas ce tafi amfana da tsarin a wannan zangon karatun, inda ta samu kaso 7.32 cikin 100 na kuɗin, sai jihar Kano a matsayi na biyu da kaso 6.72 cikin 100.

Ɗalibai a Borno sun samu adadin jimillar kuɗi da ya kai Naira 1,465,751,550.00, sai kuma Jihar Kano da ta samu Naira 1,345,709,178.

Yankin Arewa Maso yamma ne ya fi rabauta da kaso mafi yawa na kudin da gwamnatin ta biya, inda ya samu Naira 5,841,529,006
(biliyan biyar da miliyan dari takwas da arba’in da ɗaya da dubu dari biyar da ashirin da tara da Naira shida), sai Arewa maso gabas da ta samu Naira 3,941,735,487 (Biliyan uku da miliyan dari tara da arba’in da daya da dubu dari bakwai da talatin da biyar da dari huɗu da tamanin da bakwai), sai Arewa ta tsakiya da ta samu Naira 2,498,899,188 (Biliyan biyu da miliyan dari huɗu da casa’in da takwas da dubu dari takwas da casa’in da tara da dari da tamanin da takwas).

Hakan wani ƙoƙari ne na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na tabbatar da cewa ilimi ya wadata, kuma ba a bar wani matashin Nijeriya a baya ba wajen samun ilimin jami’a.

Kamar yadda shugaba Tinubu ya sha nanatawa, rashin kuɗi ba zai ƙara zama uzuri ba na rashin ilimi a Nijeriya. Wannan ya zama shiri irin sa na farko a Nijeriya da ya taimaka wajen ƙara bunƙasa karatu da ilimi a ƙasar da ma Nahiyar Afirka baki ɗaya.

By Babaji