.. Aregbesola, Malami, Fayemi, Abdullahi Adamu da wasu tsoffin minstocin Buhari a ciki
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Aregbesola, Malami, Fayemi, Abdullahi Adamu, Ministocin Buhari, da sauran ‘ya’yan jam’iyyar APC da aka fusata su bi El-Rufai zuwa SDP, yayin da suke fafutikar ganin a zaven 2027 an yi waje da Shugaban ƙasa, Bola Tinibu.
Majiyoyin da ke kusa da batun sun bayyana cewa wasu manyan jiga-jigan ‘yan siyasa da suka haɗa da tsohon minista Rauf Aregbesola, Abubakar Malami, Kayode Fayemi, da Abdullahi Adamu, na daga cikin waɗanda ke tattaunawa da El-Rufai a SDP.
Waɗannan mutane tare da wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC da ke ƙorafi, an ce suna duba yiwuwar bin El-Rufai a jam’iyyar SDP, saboda rashin gamsuwa da shugabancin APC a halin yanzu.
El-Rufai ya fice daga jam’iyyar APC ne a ranar Litinin, lokacin da ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar tare da yanke shawarar komawa jam’iyyar SDP.
A cikin wata wasiƙa da ya miƙa wa mazavarsa da ke jihar Kaduna, El-Rufai ya bayyana rashin jin daɗinsa da alkiblar jam’iyyar APC da rashin bin ƙa’idojin dimokraɗiyya da ci gaban da ya ɗauka.
A cikin wasiƙar murabus ɗin El-Rufai, ya yi tsokaci ne a kan jajircewar sa da ya daɗe a jam’iyyar APC, inda ya jaddada rawar da ya taka wajen ganin jam’iyyar ta samu nasarar lashe zabe a 2015, 2019, da 2023.
Sai dai ya ce abubuwan da ke faruwa a cikin jam’iyyar a baya-bayan nan sun haifar da rashin mutunta kimar da tun farko ta jawo shi zuwa APC.
“Na yi wa jam’iyyar APC hidima kuma na bayar da gudumawa ta don tabbatar da ita a matsayin dandalin siyasa,” inji El-Rufai.
“Duk da haka, abubuwan da suka faru a cikin shekaru biyu da suka gabata sun tabbatar da rashin mutunta ƙa’idojin dimokiraɗiyya da kyawawan ɗabi’un ci gaba waɗanda nake ƙauna.”
El-Rufa’i ya ƙara bayyana yadda yake riƙe da muƙamin Gwamnan Jihar Kaduna, inda ya yi nuni da irin ƙoƙarin da yake yi wajen ciyar da al’umma gaba, ilimi, kiwon lafiya, samar da ayyukan yi, da zuba jari a jihar.
Ya ce ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar APC, ya samo asali ne daga muradinsa na ci gaba da aiwatar da waɗannan manufofin ci gaba a kan wani tsarin siyasa na daban.
“A wannan lokacin a tafiyar siyasata, dole ne in nemi wani tsarin siyasa don neman ci gaban kyawawan dabi’un da nake so,” inji El-Rufai.
Ana kallon ficewar El-Rufai daga jam’iyyar APC a matsayin wani gagarumin ci gaba a gabanin zaben 2027.
Murabus ɗin nasa, haɗe da yiwuwar sauya sheƙa daga wasu jiga-jigan jam’iyyar APC, ya haifar da ce-ce-ku-ce game da makomar siyasar Nijeriya.
A cikin sanarwarsa, El-Rufai ya miƙa goron gayyata ga ‘yan Nijeriya da suka damu da makomar ƙasar su shiga jam’iyyar SDP.
Ya kuma bayyana jam’iyyar a matsayin tsarin dimokuraɗiyya ɗaya daya da zai iya ƙalubalantar jam’iyyar APC a zabe mai zuwa, sannan ya yi alƙawarin samar da mafita ga al’umma.
“A matsayina na dan jam’iyyar SDP, na ƙuduri aniyar samar da tsarin dimokuraɗiyya bai ɗaya domin ƙalubalantar jam’iyyar APC a zave mai zuwa,” inji El-Rufai, inda ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su haɗa kai da ƙoƙarin ganin Nijeriya ta zama fitilar ci gaba a Afirka.
A yayin da shirin ƙalubalantar shugabancin Bola Tinubu a Aso Rock ya fara kunno kai, yawan jiga-jigan jiga-jigan siyasa da ke hade da El-Rufai na nuni da cewa an samu sauyi a harkar siyasa kafin 2027.
