Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon kakakin majalisar jihar Kaduna, Yusuf Zailani ya sha alwashin yin gaba da gaba da duk wani da ya ce zai kawo wa gwamnatin Uba Sani da na Shugaban ƙasa Bola Tinubu cikas a musamman yankin Igabi dake jihar Kaduna.
Zailani ya bayyana haka ne yayin da ya amshi baƙuntar gwamnan jihar Kaduna Uba Sani da wasu makarrabansa a Rigachikum wajen yi masa ta’aziyyar rasuwa da aka yi masa.
A lokacin da yake yaba wa gwamna Uba Sani, Zailani ya ce tunda ka kafa yankin Igaba, ba ta tava kwankwaɗar romon dimokraɗiyya irin wanda gwamna Sani yake kwarara mata ba.
Bayan haka ya yaba wa gwamna Uba Sani kan rabon taki da kayan gona da ya riƙa yi wa manoman jijhar yana mai cewa hakan zai taimaka wa manoman yankin matuƙa a kakar damunan bana.
Tsohon kakakin ya bayyana cewa gwamnatocin baya sun sha alwashin gina hanyar Gadan-Gayan zuwa Kujama amma sun kasa cika alkawuran da suka dauka har zuwan gwamnati mai ci.
Ya ce tsawon shekaru 46 jama’a ke ta burin a gina wannan hanyar tun zamanin gwamnatin farar hula ta marigayi Alhaji Shehu Shagari a jamhuriya ta biyu amma ina bai tabbata ba.
”Sau ɗaya na faɗi wa Gwamna Uba Sani, kamar da wasa, sai gashi washe gari ma’aikata sun zu sun fara aiki gadan-gadan. Yanzu har sun kusa kammalawa.
Baya ga haka ya yaba da samun zaman lafiya da aka samu a jihar musamman wajen sha’anin tsaro. Da kuma sana’oi da aka kirkiro domin matasan jihar.
