Nijeriya za ta gudanar da sahihiyar ƙidaya, inji Isa Kwarra

Spread the love

Daga MAHDI MISA MUHAMMAD

Shugaban Hukumar ƙidaya ta ƙasa (NPC), Alhaji Nasir Isa Kwarra, ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa hukumar za ta gudanar da sahihin aidayar jama’a da za ta biya buƙatun da ake so a duk tsawon wannan lokaci.

Shugaban NPC ya bada wannan tabbacin ne a lokacin da tawagar kamfanin jaridar Blueprint, ƙarƙashin jagorancin Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa, Malam Salisu Umar, ta kai ziyarar ban girma a hedikwatar Hukumar da ke Abuja, ranar Talata.

Alhaji Kwarra ya ƙara da nuna kwarin gwiwa kan yadda za a fara dukkan ayyukan hukumar, wanda ya ƙunshi tsarin na’ura mai kwakwalwa, da tunkarar dukkan ƙalubalen da ke tattare da shi.

Ya ƙara da cewa, a shekarun baya lokacin da ake gudanar da ayyukan ƙidayar jama’a da hannu, an sha wuya wajen zarge-zarge da cin zarafi daga sassan ƙasar nan.

“Ya kasance al’ada ce wani sashe na aasar ya zargi ɗaya da ƙirga dabbobin gida kamar awaki da tumaki don yin ƙidayar kiwo, wani kuma ya dage cewa an ƙirga kifi ne don amfanin kansu,” inji shi.

Ya bayar da tabbacin cewa aidayar na’ura mai ƙwaƙwalwa za ta kawar da irin wannan shubuhohin.

By ukarofi