Na yi soyayya da fitattun ‘yan Najeriya bakwai – Bobrisky

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Shahararren ɗan daudu kuma sananne a kafafen sada zumunta, Idris, wanda aka fi sani da Bobrisky ya sake hargitsa kafafen sada zumunta, kuma ya dasa ayar tambaya a zukatan mutane da dama, inda ya bayyana cewa, ya yi soyayya da fitattun mutane bakwai da ‘yan Najeriya suka sani, kuma suke jin daɗin kallon su.

A cikin wani faifan bidiyo na baya-bayan nan da ya saki, wanda ba jimawa ya gama zagaya lungu da saƙon kafafen sada zumunta, Bobrisky, ya bayyana damuwa da takaicinsa kan irin rawar da rayuwar soyayyarsa ke takawa, inda ya bayyana cewa, mafi yawan masoyan nasa na masa riƙon sakainar kashi ne, ba su yi masa yadda ya kamata.

Ba tare faɗar suna ba, Bobrisky ya bayyana cewa, dangantakarsa da waɗannan sanannu kuma shahararrun mutane alaƙa ce ta gaske, duk da cewa a yanzu yana nadamar wasu daga ciki.

“Na yi soyayya da wasu fitattun ‘yan Nijeriya bakwai, ba zan ambaci sunaye ba, amma sun san kansu. Duk da ina da nadama a wani ɓangare, ina ji, Ina ma dai ban ɓata lokacina kan wasu daga ciki ba.”

Mummy of Legos kamar yadda ɗan daudun ke kiran kansa, ya ja kunnen masu aniyar tunzura shi ta hanyar maganganun da ba su dace ba, inda ya bayyana cewa, zai iya yin ƙarin bayani idan har aka tunzura shi.

Kamar dai yadda aka saba, Bobrisky ma a wannan karon ya sake hargitsa kafafen sada zumunta, inda da yawa suka kwaɗaitu da son jin sunanyen waɗannan fitattun mutanen da ya bayyana.

Bai zama sabon abu ba kasancewar ɗan daudun a tsakiyan bakin ɗinbin mutane, domin duk da kasancewar sa mai maƙiya fiye da masoya, ya kasance a layin farko da ya iya kamo zancen da ka iya firgita jama’a, har su manta da ƙiyayar da suke yi masa su fara bibiyarsa don samun amsar tambayar da ya dasa a zukatansu.

By ukarofi