Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagoranci Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ce abubuwan da wannan ɓangarori suka faɗa kamar sun shiga zuciyar gwamnatin da ne kafin su furta abubuwan da suka ƙudurta za ta cigaba da yi masu.
Gwamnan Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka a yayin taron shan ruwa da ɓangaren masana’antar fina-finan Hausa da sha’irai da kuma ƙungiyar Mawallafan Kwankwasiyya don cigaba da nuna godiyar gwamnati na ƙoƙarin kowane ɓangare.
Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce wannan gwamnati tana matuƙar godiya bisa da ganin abubuwan da ke gabata tare da sanin dukkan abinda ake gudanarwa.
“Kasancewar gwamnatin abubawa sun yi mata yawa amma dole za mu ƙara ƙaimi wajen ganin mun ninka akan abinda muke yi maku na daga kyautatawa.
“Idan kuka yi duba yanzu haka mun ɗauki wasu daga cikinku don su zo su taimaka mana ta ɓangaren zuwan mana da buƙatarku.”
Gwamna ya kuma yi nuni da irin yadda wasu ke ɗaukar sojojin Jam’iyyar NNPP ya basu ƙwaya su dinga ɓarna da kashe rayukan al’umma da barazana, amma daga gare mu mutane ne masu daraja saboda cikinsu akwai masu kwalin digiri da sauran karattuka.
“Ina ganin kuma daga ɓangaren ku zamu so muzauna daga ɓangaren kowannenku don zaƙulo waɗanda suke da ra’ayin karatu ko sana’a za mu taimaka masu su cimma nasara.”
“Haka kuma gwamnatin Kano za ta zauna da sauran Ambasadojin ƙasashen ƙetare don ganin yadda za a kawo sauyi a wannan masana’anta taku.”
Ya kuma bayyana cewa a ɓangaren tallafi kuwa akwai kuɗaɗen da gwamnati ta ware don tallafawa waɗanda suka tsufa a cikin wannan masana’anta taku, kuma za a bai wa kowane.
“Daka yabe ni na ɓata wa al’ummar Jihar Kano bisa alƙawarin da muka ɗauki alkawari na saba, ni gara a ce wani ya zage ni akan na ƙi bin ra’ayin shi.
“A nan kuma muna sanar da ku cewa mun bai wa ɓangaren masana’antar Fina finan Hausa an basu kujerun Safiya biyar (5), sannan suma Mawallafan Kwankwasiyya guda biyar sai ɓangaren Sha’irai su mun basu kujerun Hajji 3.
“Muna ƙara tabbatar wa al’ummar Jihar Kano cewa babu abinda ke gabanmu kamar kula da wannan jiha ta mu.”
A nasa jawabin Shugaban Hukumar tace fina-finai na Jihar Kano Alhaji Abba Al’Mustapha ya ce da farko suna yi wa Maigirma Gwamna ta’aziyyar rashin Abdullahi Tanka Galadanci.
Sannan ya ce sauran ‘yan uwa da abokan sana’arsu bisa ɗaukar Halisa tare da kaita asibiti don kula da lafiyarta.
Sannan Abba Ruda ya kuma buƙaci Maigirma Gwamna ya dawo masu da makarantar koyon sana’ar fina-finan Hausa da aka banzatar da su.
“Yanzu haka muna fatan Gwamna ya taimakawa wasu daga iyalan waɗanda aka rasa a cikin wannan sana’a tasu don suma su tabbatar Alhaji Abba Kabir na tare da su.
Sannan Al’Mustapha ya kuma bayyana abubuwa da daman gaske da aka yi masu na alkhairi a wannan masana’anta.
Kazalika Shugaban Kamfanin UK Entertainment Umar UK ya bayyana irin yadda wannan masana’anta tana da tarin ƙalubale na rashin jari da sauran ababaen da za su taimakawa wannan sana’a tasu.
UK ya kuma ƙara bayyana cewa duk wanda yake cewa masana’antar Fina finan Hausa na da kuɗi ƙarya yake, buƙatarsu an shine yadda gwamnatin Kano za ta shige gaba domin samun jari daga ƙasashen ƙetare.
Shi ma a nashi jawabin Shugaban Mawallafan Kwankwasiyya Alhaji Tijjani Gandu ya bayyana buƙatunsu na samar wa Mawallafan Kwankwasiyya da aikin yi da sauran buƙatun da suke da su.
A ɓangaren sha’irai da yake Jawabi a madafun su Hafiz Abdallah yace a wannan Gwamnati tana kokari wajen gudanar da ayyuka da dama.
Ya ce kuma suna tuni a kan sha’irai da suke da su don cigaba da gudanar da harkokinsu.
Haka kuma ya buƙaci Maigirma Gwamna ya samar wa wannan santa guri mai zaman kanta, inda ya kuma yi fatan sama masu bada shawara kan harkokin sha’irai ba don Al’Mustapha ya gaza ba.
Su ma daga ɓangaren masana’antar Fina-finan Hausa Alasan Kwalle ya kuma nuna farin ciki bisa ƙoƙarin da yake na ayyuka da dama.
Kwalle ya kuma buƙaci Maigirma ya ƙara samar wa marayun ƙungiyar Mawallafan Kwankwasiyya da Sha’irai.
