Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wani matashi ɗan shekara 25 mai suna Joseph Abodunrin ya kashe kansa a unguwar Dagbolu da ke ƙaramar hukumar Osogbo ta jihar Osun sakamakon tsadar rayuwa a ƙasa, lamarin da ya yi iƙirarin cewa yana dagula masa lafiyar ƙwaƙwalwa.
Jaridar ɓanguard ta ba da rahoton cewa ‘yar uwar mamacin, Abodunrin Grace ce ta tabbatar da mutuwarsa a jiya Alhamis a shafin ta na ɗ.
A cewar matar da ta bayyana shi a matsayin ɗan uwan ta da table matuƙar ƙauna, Joseph ya kasance mai ɓoye duk raɗaɗin da cikin murmushi, yana mai nuna cewa komai ya yi daidai, tare da ƙarfafa musu gwiwa.
Kafin mutuwar ta sa, an ruwaito cewa Joseph ya wallafa saƙuna a shafin ɗ na barazanar kashe kan nasa.
ɓanguard ta rawaito cewa kafin wallafa rahoton, ba’a kai ga ɗauke gawar Joseph ba duk da ya faɗi wurin da ya kashe kan nasa.
Da aka tuntuɓi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Osun, ASP Akeem Adeoye, ya shaida wa wakilin ɓanguard cewa bai san da faruwar lamarin ba, inda ya yi alƙawarin tuntuɓar su idan har aka samu ci gaba.
“Ban sani ba. Watakila dangin sa ba sa son su sanar da mu. Amma zan sanar da ku duk wani ci gaba,” inji shi.
Marigayin ya yi bikin cika shekaru 25 da haihuwa a ranar 6 ga Fabrairu, 2025.
