Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsoshon Shugaban Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya ce mulkin dimokraɗiyya ya gaza wajen kawo ci gaba a nahiyar Afrika.
Ya ce tsarin ya gaza ne saboda abin da ya ƙunsa bai zo daidai da al’adu, da yadda ake tafiyar da rayuwa a nahiyar ba, da abubuwan da mutanen nahiyar suka yi amanna da su ba.
Obasanjo ya bayyana hakan ne a Abuja, babban birnin Nijeriya, a wurin wani taron bikin cika shekaru 60 a duniya na tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilan ƙasar, Emeka Ihedioha.
Tsohon shugaban ya yi nuni da cewa idan aka kalli yadda tsohon shugaban Amurka, Abraham Lincoln, ya bayyana tsarin dimokuraɗiyya da cewa gwamnati ce ta mutane da mutane ke jagoranta domin al’umma.
Inda ya ƙara da cewa tsari ne da ake domin kowa ya amfana, ba wai wani ɓangare na al’umma ba ko wasu mutane ƙalilan ba.
Obasanjo ya kuma bayyana cewa kafin zuwan dimokuraɗiyyar ƙasashen yamma, Afrika na da nata tsarin shugabancin wanda ke kula da buƙatun kowa.
A cewarsa wannan tsarin shi ne dimokuraɗiyya, ba abin da ake kira dimokuraɗiyya ba a yau wanda ke bai wa shugabanni damar karɓar duk abin da suke so ba bisa ƙa’ida ba da kuma ta hanyar cin hanci da rashawa su ce wa mutane su je kotu idan suna da ja.
