Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyya ga Gwamnan jihar Katsina Dakta Dikko Umaru Radda bisa rasuwar mahaifiyarsa Hajiya Safara’u Umaru Baribari.
Marigayiyar, wadda ta rayu har ta kai shekaru 93, ta rasu ne a daren Asabar, inda ta bar gadon sadaukarwa da hidimar al’umma.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, shugaban ya bayyana Hajiya Safara’u a matsayin mace, wadda ta raini manyan shugabannin da suka yi fice a fannoni daban-daban.
Ya bayyana cewa, rayuwarta ta kasance cikin aminci da kuma sadaukar da kai ga yin hidima ga wasu, ɗabi’un da suka yi tasiri mai yawa.
“Shugaban ƙasa ya ce Hajiya Safara’u ta bar gadon gaskiya da hidimar al’umma wanda ya mamaye nesa da kusa.
“Shugaba Tinubu ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da ya sanya ta a Jannatul Firdaus, ya kuma jajanta wa ‘yan uwanta a wannan lokaci na bakin ciki,” inji sanarwar a wani ɓangare.
Buhari:
Haka zalika, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bi sahun gwamnati da al’ummar jihar Katsina wajen alhinin rasuwar Hajiya Safara’u Umaru Baribari.
A cikin saƙon da ya aike wa gwamnan, ta hannun mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, tsohon shugaban ƙasar ya ce “cikin tsananin baƙin ciki na miƙa saƙon ta’aziyyata ga rasuwar mahaifiyarka masoyiya, Hajiya Safara’u.
“Komai girman mutum yana buƙatar mahaifiyarsa, tunani da addu’o’in iyalina suna tare da kai da iyalinka a cikin wannan mawuyacin lokaci da muke ciki na tunawa da rayuwarta da hidimarta ga mata da sauran al’umma.
“Allah ya saka mata da kyawawan ayyukanta, da gadonta abin sha’awa ga zuriyarta da na gaba, Allah ya saka mata da Aljannatul Firdausi.”
ƙungiyar Gwamnoni:
A halin da ake ciki, ƙungiyar gwamnonin Nijeriya (NGF) ta yi ta’aziyya ga gwamna Dikko Umaru Radda bisa rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Safara’u Umaru Barebari.
A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar ta NGF, Malam AbdulRahman AbdulRasaƙ ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata, ƙungiyar ta ce “tana tunawa da rayuwar hidima, sadaukarwa, da martabar da Hajiya ta jagoranta, tare da jajantawa al’umma da gwamnatin jihar Katsina da kuma ‘ya’ya da jikokin margayiyar.”
“Addu’o’inmu da tunaninmu suna tare da Gwamna, iyalansa, da al’ummar jihar kan wannan lamari mai ban tausayi, muna kuma miƙa ta’aziyyarmu ga Hajiya Hauwa Radda, wadda matar tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa YarAdua, GCFR ce.
“Muna roƙon Allah da ya jiƙan Hajiya Safara’u, ya haskaka kabarinta, ya kuma shigar da ita Al-jannah Firdaus, muna kuma roƙon Allah da ya raya iyalin ta,” inji sanarwar a wani ɓangare.
Gwamnonin Kano, Jigawa da sauransu sun halarci sallar jana’izar:
A wani labarin kuma, Gwamnan Kano Malam Kabir Abba Yusuf da takwaransa na jihar Jigawa Alhaji Umar Namadi na daga cikin manyan mutane da suka halarci sallar jana’izar Hajiya Safara’u Umar Radda, mahaifiyar Gwamna Dikko Umaru Radda.
Taron jana’izar, wanda ya gudana da yammacin Lahadi a ƙauyen Radda da ke ƙaramar hukumar Charanchi, ya kuma sami halartar manyan jami’an gwamnati da sarakunan gargajiya.
Jami’an gwamnatin jihar da suka halarci taron sun haɗa da mataimakin gwamna, Malam Faruƙ Lawal Jobe; Kakakin Majalisar Jihar, Hon. Nasir Yahaya Daura; rakiyar ‘yan majalisa, sakataren gwamnatin jihar Barista Abdullahi Garba Faskari, ‘yan majalisar zartarwa ta jiha, da shugaban ma’aikatan gwamnati na jiha, Falaliu Bawale.
Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje:
Shugaban jam’iyyar APC mai mulki na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kuma yi wa Gwamna Radda ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Safarau’ Umar Baribari.
Ganduje, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, mai ɗauke da sa hannun babban sakataren yaɗa labaran sa, Edwin Olofu, ya ce rasuwar Hajiya Babari ta bar babban rami a zukatan ‘yan uwa da abokan arziki da kuma al’ummar jihar Katsina.
Sai dai Ganduje ya miƙa ta’aziyyarsa ga Gwamna Radda, da iyalan mamaciyar, da ɗaukacin al’ummar jihar Katsina a cikin wannan mawuyacin hali.
Ya yaba da irin gudunmawar da marigayiyar ta bayar, sannan ya yi addu’ar Allah Ta’ala ya jiƙanta da rahamarsa a cikin Jannatul Firdausi, tare da baiwa iyalai ikon jure wannan rashi maras misaltuwa.
“Tsohon gwamnan jihar Kano yana jaddada goyon bayan jam’iyyar da haɗin kan al’ummar jihar Katsina a wannan lokaci na baƙin ciki.”
